Ƙungiyar Limamai ta buƙaci Gwamna Bala ya jagoranci Bauchi shekaru takwas

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Ƙungiyar Limamai da masu wa’azi ta Jihar Bauchi ta nuna buƙatar Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya cigaba da wa’adin mulki na biyu, bayan kammala na farko a shekarar baɗi, 2023 domin ya cigaba da yi wa jama’a hidima, kafin ya hangi sama zuwa kujerar shugabancin Nijeriya.

Ƙungiyar ta yi la’akari da cewar, jihar Bauchi shekaru aru-aru ta ke bayan sa’o’in ta na ƙasar nan, biyo bayan yadda gwamnonin soji dana farar hula da suka shuɗe, bisa son zuciya suka mayar da ita ƙurar baya.

Shugaban ƙungiyar, Malam Sa’ad Mato Baba Ƙarami, a zantawar sa da manema labarai a kwanakin baya, yayi tababar cewa, zai kasance abin fari ciki da alfahari, alfanu da kishin jiha wa Gwamna Bala Mohammed yaja jagorancin sa zuwa wa’adin mulki na biyu, wato 2023 zuwa 2027 domin ya wadata jama’ar sa da ababen more rayuwa, haɗi da bunƙasa cigaba da tattalin arzikin jama’a, daman a jiha baki ɗaya.

“Haƙiƙa, wannan ƙungiya ba tana nufin bata son cigaban gwamna ba ne ya zuwa matakin shugabancin ƙasa, idan hakan shine mafi alheri a wajen Allah, amma kamar yadda ake faɗi, ‘So sone, amma son kai yafi’, don haka wannan ƙungiya zata cigaba da yiwa Gwamna Bala Mohammed addu’ar Allah ya zaɓar masa mafi alheri a cikin aiyukan sa, walau a jiha ne, ko a tarayya”.

Mallam Sa’ad Baba Ƙarami ya kuma lura da cewar, mafi yawan jama’ar jihar Bauchi hankalin su ya karkata ya zuwa ga Gwamna Bala Mohammed ya nausa zuwa gaba wa kujerar shugabancin ƙasa domin ya kwatanta ire-iren aiyuka daya gudanar a birnin tarayya ta Abuja, da ire-iren waɗanda yake yi a halin yanzu a jiha, a ɗaukacin faɗin ƙasar nan, musamman ma ta lamuran tsaro, da’a yanzu Bauchi ta kasance mafi zaman lafiyan jiha a shiyyar arewa-maso gabacin Nijeriya.

Shugaban ƙungiyar ya yabawa Gwamna Bala Mohammed bisa tsarin aiyukan sa na kawo sabbin chanje-chanje wa birnin Bauchi, musamman a fannonin kiwon lafiya, bunƙasa samar da ikimi, aiyukan gona da ababen more rayuwa kamar gina sabbin hanyoyi a cikin Bauchi da sauran sassan jiha, gina sabbin makarantun boko ga gyara wasu, samar da ruwan sha, aiyukan yi da ƙarfafa matasa domin gina sabuwar gobe.

Ƙarami ya kuma yaba wa wanda ya ɗauki nauyin gudanar da addu’o’in wata-wata na sauke Al’ƙur’ani Mai Girma da Alhaji Muttaƙa Mohammed Duguri yake yi wa Gwamna Bala Mohammed da zummar Allah yayi masa jagoranci nagari, wanyewa lafiya, da fatar alheri akan dukkan abinda ya sanya a gaba.

Malam Baba Ƙarami ya yi tuni da cewar, Muttaƙa Mohammed Duguri bai gajiya da ɗaukar nauyin wannan shiri nayin addu’o’i ba a kowane wata tunda ya fara a lokacin da wannan gwamnati ta ɗale kan ƙaragar mulki a shekara ta 2019, yana mai addu’ar Allah ya saka da alhairan sa.