Ƙungiyar Marubuta ta Arewacin Najeriya ta gudanar da taronta na shekara

*Gwamnati za ta ci gaba da haɗa hannu da marubuta don ci gaban ilimi, inji gwamnatin Katsina

*Ya kamata a duba yiwuwar koyar da wasu darussa cikin yaren Hausa – Farfesa Amale

*An karrama Ala da Balaraba Ramat a wurin taron

Daga UMAR GARBA a Katsina

Ƙungiyar Marubuta ta Arewacin Najeriya “Northern Nigeria Writer’s Summit” ta gudanar da babban taronta na shekara shekara na bana a Katsina.

Kamar kowacce shekara mutane masu tarin yawa waɗanda suka haɗa da gwamnan Katsina, Manyan malaman jami’o’i, marubuta littattafan adabin harsuna daban daban a Arewacin ƙasar nan, yan fim da kuma mawaƙa kan halarci taron.

Taken taron ƙungiyar na bana shine, ‘Yadda Adabin Gargajiya dana sauran yaruka Zai bada gudunmawa wajen magance matsalar tsaro a arewacin Najeriya’.

Baya ga tattauna yadda marubutan adabin gargajiya za su taimaka ta hanyar rubuta don shawo kan matsalar tsaro a yankin Arewa, shugabannin ƙungiyar sun kuma bada lambobin yabo ga shahararru da kuma marubuta da su ka daɗe su na bayar da gudunmawa a fagen rubutun adabi, haka zalika ƙungiyar ta ƙaddamar da wani littafi mai suna ‘Tulu’ wanda aka rubuta da harsuna daban daban na arewacin ƙasar nan.

Yayin da ake karrama Alama

Taron wanda aka kwashe kwanaki uku ana yi, ya gudana a babban ɗakin taro na sakatariyar Jihar Katsina inda daga bisani waɗanda suka shirya taron su ka zagaya da mahalarta taron wasu daga cikin wurare na tarihi a jihar.

Tun da farko da yake jawabi a wurin taron gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari wanda kwamishinan ma’aikatar yaɗa Labarai, al’adu da harkokin cikin gida, Hon. Abdulkarim Yahaya Sirika ya wakilta ya bayyana jin daɗinsa bisa jajircewar da marubuta sukayi wajen samar da litattafan nazari da bincike ga ɗaliban makarantu.

“Ilmi shi ne abu na farko da gwamnatin Jihar Katsina tafi ba wa muhimmanci, gwamnati za ta ci gaba da haɗa hannu da marubuta don ci gaban ilmi gami da cimma burin da aka sanya a gaba,” inji shi.

Duba da taken taron na bana gwamna masari ya bayyana cewar marubuta na da rawar da za su taka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma, ya kuma bada tabbacin goyon bayan gwamnatin jihar don samun nasarar abun da aka sa gaba.

Shi ma da yake nasa jawabin shugaban taron, Farfesa Idris Amale ya yaba wa marubuta musamman waɗanda ke rubuta akan adabi da sauran harsuna akan gudunmawar da suke bayarwa wajen ganin anyi riƙo da al’adu a cikin al’umma.

Farfesa Amale ya yi kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su duba yiwuwar koyar da wasu darussa cikin yaren Hausa a makarantu domin amfanin ɗalibai.

Bai tsaya nan ba sai da ya bayyana muhimmacin wallafa littattafai wajen wayar da kan jama’a kan mahimmancin abubuwan da suka shafi al’adun gargajiya, ya kuma yi kira da a qara ƙarfafa gwiwar marubuta wajen samun haɗin kai a tsakanin ‘yan Najeriya.

Mahalarta taro

A nasa jawabin, Shugaban Marubuta na arewacin Najeriya Dakta Bashir Abu Sabe dake jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina ya ce, taron an shirya shine domin ƙara ƙarfafa gwiwar marubuta da kuma nuna jin daɗin gudunmawar da suke bayarwa wajen tabbatar da riƙo da al’adun Hausa Fulani a cikin al’umma.

Dakta Sabe ya ƙara da cewa, wannan jaha tana alfahari da fitattun marubuta da suka bayar da gudunmawarsu ta hanyar rubuce rubuce don cigaban ilimi ga al’umma bakiɗaya.

Daga nan sai ya kuma yaba wa gwamna Masari da sauran masu ruwa da tsaki bisa goyon baya da haɗin kai da suke bai wa ƙungiyar tare da yin kira da ɗorewar hakan.

Farfesa Sale Abdu na jami’ar Gwamnatin Tarayyar dake Jihar Gombe wanda shine babban mai jawabi a wurin taron ya gabatar da ƙasida akan amfani da adabin gargajiya domin magance matsalar tsaro a arewacin Najeriya.

Ya bayyana cewar adabi yana ɗaya daga cikin hanyoyi na gargajiya da mutanen da ke amfani da shi don samar wa kansu tsaro da haka ne yake ganin ƙarfafa gwiwar marubuta adabi a harsunan gargajiya daban daban na arewacin ƙasar nan zai taimaka.

Sauran waɗanda sukayi jawabi a wajen taron sun haɗa da tsohon shugaban ƙungiyar marubuta ta ANA Alhaji Kabir Sani

Bayan da aka kammala gabatar da ƙasidu daban daban a ɗakin taron, an shiga ajanda ta biyu wato bayar da lambobin yabo ga shugabanni,masana, manyan malaman jami’o’i waɗanda su ka kawo cigaban adabi a arewacin ƙasar nan da kuma marubutan adabin gargajiya.

Ƙungiyar ta bawa gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari lamabar yabo, duba da yadda gwamnatin sa ke taimakawa wajen raya adabi a jihar ta hanyar haɓɓaka ilimi. kafin bayar da lambar yabo, Dakta Mukhatar Ƙasim ya bada taƙaitaccen tarihin gwamnan jihar tun daga karatunsa na firamare har zuwa lokacin da yake kan mulkin jihar a halin yanzu da kuma gudunmawar da yake bayar wa wajen cigaban marubutan adabin gargajiya a arewacin qasar da kuma qasar bakiɗaya

Sauran waɗanda suka samu lamabar yabon sun haɗa da fitaccen mawaƙi Aminu Ladan ‘Alan waƙa’

Kafin Aminu Ala ya karɓi lambar yabon sai da malam Ɗan barno ya bayyana wa al’ummar da su ka halarci taron taƙaitaccen tarihin fitaccen mawaƙin inda ya bayyana cewar Ala ya rubuta littattafai aƙalla bakwai sai dai littattafan ba su yi fice ba sakamakon wasu dalilai da ya bayar, daga nan ya ce, kasancewar Allah yai wa Aminu Ala basira mai tarin yawa sai ya daina rubuta ya koma fagen waƙa inda anan ne ya fi shahara a halin yanzu.

Farfesa Yusuf Adamu na jami’ar Bayero ne ya miƙa wa Ala lambar yabon da ƙungiyar ta ba shi.

Haka zalika ƙungiyar marubutan ta ba Hajiya Balaraba Ramat Yakubu kyautar lambar yabo.

Kafin Hajiya Balaraba ta karɓi lambar sai da Bilkisu Yusuf Ali ta bada taƙaitaccen tarihi na Hajiya Balaraba inda ta bayyana cewar Hajiya Balaraba Ramat fitacciyar marubuciya ce kuma ƙanwar tsohon shugaban ƙasar Najeriya Murtala Ramat ce.

A cewar Bilkisu, Hajiya Balaraba ta rubuta littattafai kamar irin su ‘Alhaki Kwikwiyo Ne’, ‘Wa Zai Auri Jahila’ da dai sauran su

Hajiya Balaraba ta kan kuma shirya finafinai domin kuwa ita ce ta shirya fim ɗin ‘Juyin Sarauta’, ita ce kuma ta kafa ƙungiyar marubuta mata zalla kamar yadda Hajiya Bilkisu ta bayyana.

Baya ga wannan, an ba wa Arch. Ahmed Musa Ɗangiwa lambar karramawa. Ɗan giwa yana ɗaya daga cikin waɗanda su ka nemi tsayawa takarar gwamnan Jihar Katsina a zaɓen fidda gwani da jam’iyyar APC ta gudunar, shi ne tsohon shugaban bankin bada lamunin gidaje na ƙasa.

Alhaji Na sudan wanda ya wakilci Ɗan giwa ya bayyana cewar Arch. Ɗan giwa ya daɗe yana bayar da gudunmawa ga adabin gargajiya ta yadda yakan shirya gasar marubuta adabi domin haɓɓaka rubutan littattafan adabi a tsakanin al’umma.

An kuma ba wa tsohon shugaban gidauniyar tallafin man fetur PDTF Muttaƙa Rabe Darma lambar yabo duba da yadda yake tallawa adabi a Jihar Katsina ta hanyar ɗaukar nauyin ɗalibai da kuma ba su horo.

Fitaccen ɗan jarida malam Ɗan juma Katsina ne ya karɓi lambar yabon a madadin Muttaƙa Rabe Darma.

Sa’ilin da ake karrama Ramat

Sauran waɗanda aka ba wa lambar yabon su ne; Farfesa Sa’idu Gusau na jami’ar Bayero da ke Kano, sai kuma Farfesa Maria Ajiba, sai kuma Farfesa Albishir mai sharhi a kafafen yaɗa labarai da kuma Farfesa Sale Abdu da ke jami’ar Gwamnatin Tarayyar a Gombe.

Aminu Ladan Ala shi ne yai jawabin godiya a madadin waɗanda ƙungiyar ta karrama da lamabar yabo inda ya bayyana cewar karramawar da akai ma su zata ƙarfafa masu gwiwar cigaba da raya adabin gargajiya a arewacin Najeriya.

Daga ƙarshe Ala da sauran mawaƙa sun nishaɗantar da mahalarta taron.