Ƙungiyar masu maganin gargajiya ta yi sabbin naɗe-naɗe

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Ƙungiyar masu maganin gargajiya ta ƙasa, wato ‘National Union of Medical Herbal Practitioners’ ta naɗa sanannen mai maganin gargajiyan nan wato Dakta Kabiru Mohammed wanda aka fi sani da Dakta Naborgu a matsayin sabon shugabanta na rikon ƙwarya.

Babban taron naɗin wanda aka gudanar a hedikwatar ƙungyar na ƙasa da ke Kuje a Abuja ya samu halartar jiga-jigan ’ya’yan ƙungiyar daga sassa daban-daban a ƙasar nan baki ɗaya.

A jawabin alƙalin ƙungiyar Alhaji dokta Mustapher Abgaje bayan ya gabatar wa sabon shugaban riƙon takardar shaidar kama aiki ya kuma sanar cewa sauran mambobi da za su yi aiki tare ƙarƙashin jagorancin sabon shugaban sun haɗa da Adamu Umar Baffa (Sakatare) da Prince Adeagbo O. Suleiman (P.R.O) da Alhaji Dakta Ibrahim Ogunsiye (BOT) da Hajiya Adama Suleiman (Uwar qungiya), inda ya buƙace su da su tabbatar sun sauke wannan nauyi da ke wuyarsu yadda ya dace.

A nasa ɓangaren da ya ke zanta da wakilinmu jim kaɗan bayan an gabatar masa da takardar shaidar, sabon shugaban ƙungiyar na riƙon ƙwarya Dakta Kabiru Mohammed ya gode wa mambobin ƙungiyar baki ɗaya dangane da zaɓinsa da suka yi musammsn Alhaji Babangida Usman Matazu wanda ya fara gabatar wa ƙungiyar sunansa a matsayin wanda ya dace ya shugabanci ƙungiyar na riƙon ƙwarya, inda ya yi alƙawarin yin duka mai yuwa wajen haɗa kan ’ya’yan ƙungiyar a kasa baki ɗaya.

Ya ƙara da cewa, zai tabbatar bai ba su kunya ba.