Ƙungiyar R-WIN-WIN ta gudanar da taron shawartawa kan takarar Tunubu

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

Ƙungiyar matasa masu neman cigaba a harkar siyasa mai suna R-WIN WIN, ta gudanar da taron tattaunawa da kuma neman shawarwari a game da siyasa da kuma kakar zaɓen shekarar 2022 da ta ke tunkarowa.

Taron wanda aka gudanar da shi a ranar Asabar 5 ga Fabrairu, 2022 a wajen shirya taro na Hajjo Event Center da ke titin Audu Baƙo a cikin garin Kano, ya samu halartar matasa masu yawan gaske da suka haɗar da mata da maza.

Tun da farko da ya ke bayanin manufar taron da Kuma tafiyar ƙungiyar ta su. Shugaban Ƙungiyar, Auwal Abdu Dankano. Ya Bayyana cewa, sun kafa ta ne saboda kare muradun Jam’iyyar su ta APC, domin ya zamo matasan su su samu aikin yi.

Wanda Kuma wannan taro ya zama an shirya shi ne bayan taron da suka saba yi duk ƙarshen sati. Don haka ya haifar da wannan taro domin su tattauna a Kan wanda ya kamata su sa a gaba wajen zaɓen da za a yi mai zuwa, don haka a matsayin mu na matasa masu son ci gaba muna buƙatar tattaunawa da neman shawarwari, domin samar da Shugaban da ya dace da ci gaban ƙasar mu baki ɗaya, don haka Ina fatan wannan taron da muka shirya, ya zama sila ta samar da Shugaban da Nigeria za ta yi alfahari da shi.

Shi kuwa a nasa jawabin. Babban baƙo mai Jawabi a wajen, Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano Alhaji Rabiu Sulaiman Bichi, ya fara da cewar.

“A wannan rana za mu tattauna matsayin mu na ’yan ƙasa Kuma ’yan Jihar Kano in da tattaunawar za ta kalli samo wanda zai gaji Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, kuma muna fatan wanda shi mu ke tunanin idan Allah ya sa ya kai ga za a kai ga fitar da gwani.”

Ya ci gaba da cewa, “idan muka duba an yi gwagwarmaya. Amma ba a kai ga nasara ba sai da aka sawo Bola Ahmad Tunubu a 2015 da kuma 2019, don haka a yanzu mu ke ganin shi ne ya kamata ya ɗora. Saboda ana son Shugaba ya zamo yana da wasu muhimman halaye, don haka shi Bola Tunubu Shugaba ne wanda ya san hanya Kuma ya san yadda a ke mulki. Don haka idan muka duba shi ba za a yi masa girin kuɗi ba, domin shi babar sa mai kuɗi ce don haka ba zai yi  kwaɗayin kuɗi ba, sannan shi akanta ne a kamfanin mai don haka ba a yi masa gorin abin duniya ba.”

Ya ƙara da cewar, “idan muka duba abin da ya shafi mulki kuwa, kowa ya ga yadda Tunubu ya gyara jihar Legas a lokacin yana matsayin Gwamna, wanda iya jagorancinsa ne ya sa har yanzu a kan manufarsa a ke tafiya a jihar, kuma duk wanda ya nemi ya sauya, to mutanen jihar ma ba za su yarda da shi ba. Don haka muke da burin ya kasance a matsayin shugabann ƙasa a zaɓe na gaba.”

Shi ma a nasa jawabin, Ambasada Aliyu Lawal Saulawa ya bayyana Bola Ahmad Tunubu a matsayin mai kishin ƙasar da ya kamata a ce kowa ya amince da shi saboda ba shi da nuna wariya da  ƙabilanci a lokacin da yana Gwamna ya naɗa ’yan kowanne ɓangare na ƙasar na a cikin Gwamnatin sa ta jihar Legas, don haka ya ku ke ganin idan ya zama Shugaban ƙasa.

Ita ɗaya daga cikin mata matasan da su ke yunƙurin samar da ci gaban matasa. Hajiya Maryam Hali ta bayyana Muhimmancin samar da shugaban da zai kawo ci gaban matasa, don haka a cewar ta a yanzu babu wanda zai samar da wannan ci gaban sai Bola Ahmad Tunubu, don haka ne su ke fatan ya kasance a matsayin Shugaba a zaɓe mai zuwa.

Ita ma a na ta Jawabin Hajiya Binta Rabiu Spikin ta bayyana cewar yanzu siyasa ta canza, don haka dole ya zama matasa sun shiga siyasar cikin tsari ba wai a ba ku taliya da sabulu ba, don haka mu gane sai wanda zai samar da aikin yi, saboda haka mu yi amfani da damar mu kada ya zaba an zo taron siyasa an ba mu Kaza da Kifi, kuma idan an ci zaɓe a manta da mu. Taron dai ya gudana cikin tsari kuma an yi an gama lafiya.