Ɓata-gari sun far wa jami’an Kwastam a Ogun

Daga AISHA ASAS

Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Ƙasa a Jihar Ogun, ta ce wasu ‘yan fasa-ƙwauri sun kai wa jami’anta hari a bakin aiki a Larabar da ta gabata inda aka yi musayar wuta wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar wani mazaunin ƙauyen Ohunbe mai suna Tunde Alabe.

A cewar hukumar an yi arangamar ne a lokacin da jami’an kwastam suka yi ƙoƙarin daƙile fasa-ƙwaurin fetur zuwa ƙetare da masu harkar suka so yi.

Ta ce ɓata-garin sun far wa jami’anta ne ɗauke da muggan makamai da suka haɗa da sanduna da bindigogi da dai makamantansu.

Lamarin ya yi sanadin datse hanyar Oja-Odan/Obelle inda ‘yan tada-zaune-tsayen suka banka wuta a shingayen bincike na kwastam da na takwarorinsu a yankin Olajogun zuwa Hanger da Ohunbe duka a jihar Ogun.

Kayayyakin da da ‘yan tada-ƙayar-bayan suka lalata yayin arangamar sun haɗa da motocin aiki da gine gine da muhimman takardu da dai sauransu.

A bisa wannan dalili ne shugaban hukumar na shiyya, Compt. Peter Chado Kolo, ya lashi takobin gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin tare da tabbatar da masu hannun cikin hatsaniyar sun fuskanci hukunci.