Ɓatagari sun halaka gyatuma bayan sun yi mata fyaɗe a Ondo

Wasu ɓatagari da ake zargin Fulani makiyaye ne, sun yi taron dangi wajen yi wa wata mata mai suna Mrs Roseline Joguntan fyaɗe sannan suka halaka ta bayan haka a ƙauyen Igbokoda da ke cikin yankin ƙaramar hukumar Ilaje, jihar Ondo.

Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa, an aikata wa matar wannan ɗanyen aiki ne a gonarta sa’ilin da ta je ɗibar ‘yan’yan itatuwa kamar yadda ta saba tare da ɗaya daga cikin ‘ya’yanta.

Majiyar jaridar ta ce, “Bayan da marigayiyar ta ɗibi kwandon farko na ‘ya’yan itatuwan ne sai ta buƙaci ‘yarta ta ɗauka ta kai gida, ko da yarinyar ta dawo ba ta tarar da mahaifiyarta ba, daga bisani ta gano ta kwance a mace cikin ciyawa.

“Daga bisani mijin matar, Mr Joguntan ya kai rahoton aukuwar hakan ga ofishin ‘yan sanda bayan da ya je neman matarsa a gona ya gano ta mace cikin jini.”

Mazauna yankin sun yi zargin Fulani makiyaya da suka mamayen yankin ne suka aikata wannan aika-aikar.

Mai magana da yawun ‘yan bangan yankin Ilaje, Prince Emorioloye Owolemi, ya koka kan yadda ake samun yawan aukuwar halaka mutane a yankin a lokutan baya-bayan nan, tare da miƙa ƙoƙon bara ga gwamnatin jihar kan a kawo musu ɗauki.