Ɗakunan gwajin ƙwayoyin hallitu da Amurka ta kafa a ƙasashen duniya sun haifar da babbar illa ga tsaron bil Adam

Daga AMINA XU

A ranar 10 ga wata, hukumar tsaron ƙasar Rasha ta fitar da wasu takardun da ta samu daga ma’aikatan dakunan gwajin da Amurka ta kafa a Ukraine, inda suka fayyace aikin gwajin da Amurka da ƙawayenta na NATO suke yi a Ukraine ta fannin nazarin makamai masu guba, ciki har da yaɗuwar cutar murar tsuntsaye ta tsuntsayen da suke ƙaura, da kwayar cutar dake iya yaɗuwa daga jemage zuwa Bil Adama da sauransu.

Ban da wannan kuma, a ƙarshen watan Fabrairu, cikin gaggawa ne ofishin jakadancin Amurka dake Ukraine ta soke bayanan da ke shafar dakunan gwajinta a shafinta na yanar gizo. Sai dai wannan wani ɓangare ne kawai na ɗakunan gwajin ƙwayoyin hallitu da Amurka ta kafa a ƙasashen ƙetare.

An ce, gaba ɗaya Amurka ta kafa irin dakunan gwajin fiye da 300 a ƙasashe 30, ciki hadda ƙasashen nahiyar Afrika da yankin gabas ta tsakiya da ƙasashen kudu maso gabashin Asiya da yankunan tsohuwar tarayyar Soviet da sauransu, har ma an samu ɓarkewar annoba masu yawan yaɗuwa a wasu yankunan da ɗakunan gwajin suke.

To mene ne dalilin Amurka na kafa irin waɗannan dakunan gwaji a ƙasashen waje? Ya kamata Amurka ta gabatar da cikakken bayani game da ɗakunan don kwantar da hankulan mutanen duniya.

Mai zane: Amina Xu