Ɗan acaɓa ya lashe zaɓen majalisar wakilai a Kudancin Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An bayyana wani ɗan acaɓa, Donatus Mathew a ƙarƙashin jam’iyyar LP a matsayin wanda ya lashe zaɓen ɗan takarar majalisar wakilai ta Kaura da ke Jihar Kaduna.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen a jiya, jami’in zaɓen, Farfesa Elijah Ella, ya ce Mathew ya samu ƙuri’u 10,508 inda ya doke ɗan takarar jam’iyyar PDP, Gideon Lucas Gwani wanda ya zo na biyu da ƙuri’u 10,297.

A cewar rahotanni, Mathew ya taɓa zama Kansila amma wahala ta tilasta masa zama ɗan acaɓa. An kuma ce shi ɗan Nijeriya ne mai gaskiya kuma mai riƙon amana.

Ya ce, ɗan takarar APC ya zo na uku da ƙuri’u 9,919, yayin da na jam’iyyar NNPP ya samu ƙuri’u 5,354 ya zo na huɗu.

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan bayyana wanda ya lashe zaɓen, zaɓaɓɓen ɗan majalisar, Donatus Mathew, ya godewa masu zaɓe bisa amincewar da aka bashi na ya wakilce su a zauren majalisar.

Sai dai ya nemi goyon baya da haɗin kai daga jama’a tare da yin alƙawarin ci gaba da tafiya da kowa domin cimma nasarar da ake buƙata.

Da yake mayar da martani kan sakamakon, ɗan majalisar mai ci wanda kuma shi ne ɗan tsiraru a majalisar wakilai, Gideon Lucas Gwani ya taya zaɓaɓɓen ɗan majalisar murna tare da yi masa fatan alheri.

Ya buƙaci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu, su kuma amince da sakamakon zaɓen, ya ce, domin Allah ne ke bayarwa kuma yake karɓan mulki.