Ɗan Chana ya fallasa abubuwan ta’ajibi a shari’ar kisan Ummita

*Ba na roƙon kada a kashe ni, inji shi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗan ƙasar Chana ɗin nan mai suna Frank Geng Quangrong mai shekaru 47 da ake tuhuma da laifin kashe masoyiyarsa, jiya Alhamis ya sake faɗa wa kotu a Kano cewa bai taɓa niyyar kashe budurwarsa ‘yar Nijeriya mai suna Ummukulsum Sani ‘yar shekara 22, da aka fi sani da Ummita ba.

Wanda ake tuhumar, mazaunin Railway Quarters a Kano, ana tuhumar sa da laifin kisan kai.

Da lauyan gwamnati, Musa Lawal ke tambayar dalilin sa na zuwa gidan su Ummita ba tare da gayyata ba, kuma har ta aiko mishi da faifan bidiyonta? Sai ɗan Chanan ya kaɗa baki ya ce shi bai yi niyyar kasheta ba.

“Ban yi niyyar kashe Ummukulsum ba, kuma ba na son a kashe ni. Ta raunata ni a al’aurata kuma ba zan iya nunawa kotu ba, saboda ya saɓa wa al’adun ƙasar Sin, kuma ni Musulmi ne.

“A wannan rana mai muni, sai ta kira ni ta WhatsApp ta ce in kawo mata karenta mai suna Charlie.

“Da isa ta gidan su, bayan ta ƙi ɗaga wayata, sai na aika mata da saƙon tes, daga baya mahaifiyarta (Fatima Zubairu (Pw1)) ta buɗe ƙofa, na shiga domin na ɗauko Charlie.

“Ban yi magana da mahaifiyar marigayiyar ba saboda ba ta jin Turanci kuma ni ba na jin yaren Hausa,” inji Frank.

Haka dai aka riƙa titsiye ɗan Chana a kotun bayan kotun ta karɓi shaidun da aka kawo a kan kisan.

Daga nan sai Alƙali Sanusi Ado Ma’aji ya ɗage ci gaba da shari’ar sai ranakun 29 da 30 ga watan Maris.