Ɗan dimokuraɗiyya na gaske ba ya ƙin sakamakon zaɓe ko da an tafaka maguɗi – Tinubu

Daga WAKILINMU

Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewar ɗan dimokuraɗiyya na gaske ba zai ƙi karɓar sakamakon zaɓe ba ko da kuwa an tafka maguɗi a zaɓen.

Tinubu ya faɗi haka ne a matsayin martani ga ‘yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun PDP da Labour, Atiku Abubakar da Peter Obi.

Tun ana tsaka da tattara ƙurin zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana, Atiku da Obi suka buƙaci a soke zaɓen.

Sun bukaci hakan ne bayan da suka yi zargin an tafa maguɗi sakamakon rashin amfani da na’urar BVAS.

Da yake amsa tambayar manema labarai bayan ziyarar da ya kai wa Shugaba Muhammmadu Buhari a Daura, Jihar Katsina a ranar Laraba, Tinubu ya ce gina ƙasa ita ce gaba da komai.

Daga bisani, Tinubu ya yaba wa Shugaba Buhari kan yadda ya bai wa sha’anin dimokuraɗiyya muhimmanci a Afirka.