Ɗan jarida na neman diyyar miliyan N100  bisa naushin da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai ya yi masa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

A yayin da ake bikin ranar cin zarafin ‘yan jarida ta duniya a duk ranar 2 ga Nuwanban kowace shekara, wani ɗan jarida a Kano ya fuskancin cin zarafin a wajen shugaban masu rinjaye na Majalisar Tarayya mai makiltar Tudun Wada da Dogowa Hon. Alasan Ado Doguwa.

Lamarin dai ya faru ne bayan Doguwa ya kira taron ‘yan jarida a gidansa domin maida martani akan rikicinsu da ɗan takarar Mataimakin Gwamnan Kano Hon. Murtala Sulen Garo. 

Ɗan jaridar mai suna Abdullahi Yakubu na Jaridar Leadership ya garzaya kotun Gyaɗi-gyaɗi ƙarƙashin jagorancin Halima Kurawa, inda ya nemi kotun ta ƙwato masa haƙƙinsa na naushinsa da Hon. Alasan Ado Doguwa ya yi a lokacin da ya yi taron manema labarai a gidansa.

A cewar Abdullahi kunnesa fa ba ya ji sosai sai sama-sama, inda ya garzagaya kotun tare da neman kotun ta karvar masa Naira miliyan 100, ta kuma talasta shi rubuta takardar bada haƙuri.

Saura da me? Abin jira a gani shine amsa gayyatar da Hon. Doguwa zai yi a gaban ‘yan sanda na shiyya ta 1 da ke Sharaɗa a Kano.

Ricikin cikin gida dai na ta yin ƙamari a cikin Jam’iyyar APC a Kano, lamarin da masu sharhi a kan siyasa ke ganin zai iya shafar jam’iyyar a zaɓen 2023.