Ɗan Majalisa ya ɗauki nauyin horas da mutane 387, kasuwanci a Ƙauru

Daga MOH BELLO HABIB a Zariya

Wani Ɗan Majalisar wakilai na tarayyar Nijeriya mai wakiltar mazaɓar Ƙauru cikin jihar Kaduna, Honorabul Mukhtar Zakari Isa Chawai ƙarƙashin kulawar Hukumar Sanya Ido a kan kayayyakin dake amfani a Nijeriya (Nigeria Bio safety Management Agency) ya ɗauki nauyin horas da matasa 387 sanin dabarun kasuwanci a mazaɓarsa.

Ɗan majalisar ya faɗi wannan batu a yayin rufe taron horas da wasu ƙarin matasan har su 27 na tsawon kwanaki 3 da ya ɗauki nauyin gudanarwa a ɗakin taro dake garin Ƙauru ranar Lahadin da ta gabata.

Ya ce, wannan horaswa ita ce karo na 7 a jerin waɗanda aka yi a baya. Inda ya bayyana cewa, idan an haɗa da waɗannan, a jimlace, ya ɗauki nauyin koyar da matasa maza da mata Har 387 dabarun kasuwanci tare da ba su kayayyakin sana’o’i wanda zai ba su damar samun Jari domin fara kasuwanci da suka zaɓa wa kawunansu.

Chawai ya ce, “mun yi tunanin ba su kayan sana’o’i domin samar wa kansu jari don ƙarfafa musu gwiwa duba da lakarin da halin da ake ciki. Wasu idan an ba su tsabar kuɗi saboda su yi jari, za su iya kashewa. Amma kayan sana’a zai fi taimakawa saboda mu burinmu shi ne, mu ga sun kafu.

“Za mu ci gaba da wannan tsari saboda mu tallafa wa tattalin arzikin jama’armu da Kuma ƙaramar hukumarmu ta Ƙauru.”

Da take sanya albarkar bakinta, wata jami’a a Hukumar Sanya ido a kan kayayyakin masurufi ta ƙasa, uwargida Victoria Dogari ta yi kira ga waɗanda aka horas din da su yi amfani kayayyakin sana’ar da aka basu ta hanyoyin da suka kamata domin samar wa kansu da jari don fara kasuwanci kamar yadda ɗan majalisar ya tsara. Saboda waɗanda za su biyo baya, su ma su yi koyi da haka.

Ta ƙara da cewa, yin hakan zai haɓaka tattalin arzikin ƙaramar hukumarsuu da kuma cigaban alumma.

Haka nan Victoria Dogari ta yaba wa ɗan majalisar a kan wannan hangen nesa da tunanin da ya yi.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, waɗanda aka horas ɗin a baya-baya su 27 an ba su kayayyakin sana’o’i da suka haɗa da babura ƙirar TVS waɗanda aka fi Sani da Boko Haram guda 20, da Injinan ba da hasken lantarki guda 9 da Kuma babura masu ƙafa uku watau Keke nafef guda 3 ko a-dai-dai-ta-sahu.

Da take magana da yawu waɗanda suka amfana, ɗaya daga cikinsu,Talatu Bello ta bayyana jin daɗinta game da wannan tagomashi da ɗan majalisar ya yi musu. A cewar ta, wannan ɗan majalisa shi ne na farko da ya yi irin wannan kyakkyawan tunani.

Don haka, ta yi kira ga sauran waɗanda suka amfana da kada su ba ɗan majalisar kunya. Kuma su alkinta kayayyakin da aka ba su a matsayin jari domin su ne za su amfana.