Ɗan majalisa ya nemi a yi watsi da ƙudirin hana acaɓa a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗan Majalisar Wakilai ya nemi a yi watsi da ƙudirin da ke neman kafa dokar haramta sana’ar acaba a faɗin ƙasar nan.

Yayin zamanta na ranar Talata, ɗan majalisa mai wakiltar Jigawa a Jam’iyyar APC, Abubakar Yallemen ne ya gabatar da ƙudurin, inda ya buƙaci su yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da shirin da take yi na haramta sana’ar acaɓa a faɗin ƙasar nan.

Jaridar Manhaja ta ruwaito cewa, ɗan majalisar ya buƙaci a tabbatar da an samar da shirye-shiryen da za su taimaka wajen rage wa ‘yan qasa raɗaɗin haramta acava kafin ɗaukar matakin hanawa.

Ya ƙara da cewa, idan ya kama a haramta sana’ar ta acaɓa, ya zamana hakan ya shafi yankunan ƙananan hukumomin da suke fama da ‘yan ta’adda da kuma harkokin haƙar ma’adinai ne kaɗai.

Sa’ilin da yake gabatar da ƙudirin nasa ga majalisar, Yallemen ya nuna cewa muddin aka haramta sana’ar acava hakan zai jefa rayuwar miliyoyin ‘yan Nijeriya cikin halin rashin aikin yi, wanda a cewarsa hakan zai zama ƙarin matsala ga ƙasar da ke fama da talauci da kuma zaman kashe wando.

Ya ce wajibi ne yayin da ake shirin haramta acava a matsayin wani mataki na magance matsalar tsaro, a kuma yi la’akari da walwalar ‘yan ƙasa kamar yadda Sashe na 14(2)(b) na Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa ya tanadar.

Sai dai kuma, Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Honorabul Ahmed Wase, ya jaddada buƙatar ‘yan majalisar su mara wa Gwamnatin Tarayya baya wajen shawo kan matsalar tsaron da ta addabi ƙasar.