Ɗan shekara 17 ya ƙirƙiri na’urar saƙago a Kano

Wani matashi ɗan asalin Jihar Kano mai shekara 17 ya ƙirƙiro na’urar saƙago wanda ake kira da ‘Robot’ a Turance, da ya ke sarrafata ta hanyar motsi da hannunsa.

Matashin, mai suna Isah Barde dai wanda bai jima da kammala karatun Sakandare ba, ya ƙera na’urar ce ta hanyar amfani da kwalaye da ƙarafa.

Isah dai ya bayyana cewa, yana da burin zama kwarare a fannin nazarin fasahar saƙago, duk da cewa iyayensa masu ƙaramin larfi ne.

A zantawarsa da manema labarai, matashin ya ce, tsawon shekara uku ya ɗauka yana haɗa na’urar, wacce ya bayyana a matsayin wani ɓangare burin rayuwarsa, duk da yanayin rashin kuɗin da ya ke ciki.

Isah dai na sarrafa na’urar ce ta hanyar motsi da hannayensa.

Ya ce, “Na haɗa wannan saƙago ne da takardu da kwalaye da tayar mota har ma da itace.

“Wasu sayowa na yi a kasuwar Jakara, wasu kuma mutane na roƙa suka ba ni, kamar na’urar busar da gashi da ta lalace, na samo ta ne na kwance ta na kwashi abubuwan da nake buƙata,” inji shi.

A nasa ɓangaren, mahaifin yaron, Auwal Barde, ya ce, yana alfahari da ɗan nasa, sai dai yana fama da rashin kuɗin da zai iya cika masa burin nasa.

“Kiwon kaji na ke yi na sayar, don haka ba ni da halin ɗaukar nauyin karatunsa, amma zan yi farin ciki idan aka samu wanda zai taimaka mana ya yi hakan,” inji mahifin Isah.

Shi ma dai wani ɗan uwan Isa mai suna Muhammad, ya ce, “nan gaba ba mu san me zai ƙirƙira ba da ƙasarmu za ta yi alfahari da shi, shi ya sa da na ga yana nuna alamun watsar da burinsa na ke ba shi kwarin gwiwa.”

Iyayen na sa sun ce tun ɗan nasu yana da shekara takwas ya fara bayyana soyayarsa da ƙere-ƙere.