Ɗangote da BUA za su amfana da tallafin jarin sukari daga CBN

Daga AMINA YUSUF ALI

Ana sa ran kamfanonin sukari na Ɗangote da BUA da sauran wasu kamfanonin sukarin za su amfana da jarin Dalar Amurka miliyan 73 a matsayin tallafin gwamnatin tarayya ga sashen samar da sukari a ƙasar.  

Babban Bankin Nijeriya (CBN), da yawun gwamnatin tarayya, zai  ware Dalar Amurka Miliyan 73 domin ƙara bunƙasa harkar samar da sukari a ƙasar ta fuskar kayan aiki da injinan sarrafa sukarin da za su wadaci masana’antun sukari da suka kai faɗin hekta dubu goma. 

Ministan masana’antu, Mista Niyi Adebayo, shi ya bayyana haka a Abuja ranar litinin ɗin da ta gabata. Inda ya bayyana cewa, za a nemi hekta dubu na filin masana’antu daga wuraren samar da sukarin guda shida a Arewacin Nijeriya. Domin ƙara bunƙasa samar da suga a faɗin ƙasar, inji shi. 

Inda ya bayyana cewa: “Babban muradinmu shi ne mu ɗauki nauyin samar da kayan aikin sarrafa sukari a masana’antun sukari masu faɗin hekta dubu goma wacce za a nemo a cibiyoyin samar da sukari guda shida waɗanda suke a garuruwan: Numan ta jihar Adamawa, Sumti ta jihar Neja, Lafiyagi da Bacita dukka a Jihar Kwara, sai kuma garuruwan Toto da Tunga dukkansu a jihar Nasarawa” inji shi. 

A wani jawabi nasa a shafin yanar gizo, shi ma Ɗangote ya bayyana cewa, in dai har za a yi aiki da wannan tsarin da aka zo da shi, to tabbas Nijeriya za ta dinga samun rarar Dalar Amurka miliyan 600 zuwa dala miliyan 700 a wajen kuɗaɗen da take kashewa wajen canjin kuɗi kowacce shekara. 

A cewar Ministan, Gwamnatin tarayya da ma ta samar da wannn tsarin ne domin ƙasar Nijeriya ta samu damar dogaro da kanta wajen samar da sukari wanda zai ishe ta amfanin cikin gida sannan ta zama mai fataucin sukarin zuwa ƙasashen ƙetare abinda a cewarsa zai sa ta samu rarar maƙudan kuɗaɗen da take kashewa wajen canjin kuɗaɗen ƙasashen waje don shigo da sukari daga ƙasashen na ƙetare.