Ɗangote ya zama na 117 a jerin masu kuɗin duniya

Shugaban Rukunin Kamfanin Ɗangote, Aliko Dangote, ya zama na117 daga jerin masu kuɗin duniya, kamar yadda ƙididdigar jaridar Bloomberg ta nuna.

Ƙididdigar na bibiyar masu kuɗin duniya ne kulli yaumi sannan bayan haka a fitar da jerin sunayen su gwargwadon yadda suka fi juna arziki tare da wallafa matsayin kowannensu a shafinsa na intanet.

Ƙididdigar ta nuna ana tattara bayanan da kuma sabunta su dangane da masu arzikin ne a-kai-a-kai, inda a wannan karo Ɗangote ya zama na 117 da ƙarfin arzikinsa ya kai Dala nilyan $17.8.

Ƙididdigar ta Bloomberg ta nuna Elon Musk shi ne ya zo na ɗaya a jerin masu kuɗin duniya da kuɗi Dala biliyan $194. Yayin da Jeff Bezos ke biye da shi da arzikin da ya kai Dala biliyan $194.

Na ukun su shi ne Bernard Arnault mai karfin arzikin da ya kai Dala bilyan  $174. Matsayin da hamshaƙin ɗan kasuwar nan kuma mamallakin kamfanin Microsoft, Bill Gates, ya taka a baya-bayan nan amma ya rasa matsayin saboda miƙa wa tsohuwar matarsa wani kaso daga dukiyarsa.

Sannan mamallakin kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg, shi ne ya ɗare matsayi na biyar a tsakanin masu kuɗin duniya da ƙarfin arzikin da ya kai Dala biliyan $135.