1 ga Mayu sabon albashi mafi ƙaranci zai fara aiki – Gwamnati

*Ba mu amince da ƙarin albashin kashi 35 ba — NLC

Daga BSHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta ba da tabbacin cewa sabon albashi mafi ƙaranci zai fara aiki daga 1 ga Mayu.

Kodayake, Gwamnatin ta ce kwamitin da ke da ruwa da tsaki kan batin ƙarin albashin bai kammala aikinsa ba tukuna.

Ƙaramin Ministan Ƙwadago, Nkeiruka Onyejeocha, ita ce ta yi wannan babayin a wajen taron bikin Ranar Ma’aikata da aka shirya ranar Laraba a Abuja.

Ta ce abin takaici ne ƙarin albashin bai kammalu ba zuwa wannan lokaci, amma cewa ana ci gaba da tattaunawa domin tabbatar dukkanin bayanai sun haɗu nan ba da daɗewa ba.

Idan za a iya tunawa, ƙungiyoyin NLC da TUC sun syi kira ga gwamnati mai ci ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu sau tari kan ta duba ta yi wa ma’aikata ƙarin albashi.

Kuma ko a baya-bayan nan, an ji inda NLC ta buƙaci gwamnatin da ta sanya mafi ƙarancin albashi zuwa N615,000 domin bai wa ma’aikata damar yin rayuwa cikin walwala.

Ƙungiyar ta ce, N30,000 da ake biyan ma’aikata a matsayin mafi ƙarancin albashi a halin yanzu bai isa kula da buƙatun ma’aikaci.

Ta ƙara da cewa, ba ma duka gwamnonin jihohi ke biyan N30,000 ɗin ba.

A nasa ɓangaren, Shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero, ya ce ƙarin albashi da kashi 35 da Gwamnatin Tarayya ta ce yi hakan ba zai saɓu ba. Yana mai cewa, N615,000 shi suke buƙata gwamnati ta biya a matsayin mafi ƙarancin albashi don walwalar ma’aikata.