10-10 Initiatives ta buƙaci kotu ta yi wa Atiku Abubakar adalci

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU a Jos

Ƙungiyar magoya bayan Wazirin Adamawa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar PDP a Babban Zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar, mai laƙabi da 10-10 Initiative for Atiku Abubakar, ta buƙaci Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Shugaban Ƙasa da ya gabata da ta tabbatar da ta yi nazarin hujjojin da ɗan takarar da suke goya wa baya ya shirya gabatarwa yadda ya kamata, kuma a yi masa adalci, don cigaban dimukraɗiyya da kiyaye martabar ɓangaren shari’a.

Ƙungiyar ta yi wannan kira ne a cikin saƙon ta na Barka Da Sallah da ta aike wa ýan Nijeriya albarkacin bukukuwan ƙaramar Sallah da ta gudana, wanda ke ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar na ƙasa, Malam Abdulhadi Abdullahi Cokali, wanda kuma ya bayyana yabawa da jinjina ga ýan Nijeriya bisa goyon baya da zaɓen da suka yi wa Wazirin Adamawa a Babban Zaɓen Shugaban Ƙasa na 2023.

Malam Abdulhadi Cokali ya bayyana cewa, irin ƙauna da goyon bayan da ýan Nijeriya suka nuna wa Atiku Abubakar da Jam’iyyar PDP ya ba ta damar samun gagarumar nasara, duk da maguɗin da suke zargin an tafka a wasu wurare, da saɓa wa dokokin zaɓe da aka yi, wanda ya sa yanzu haka ɗan takararsu ke neman haƙƙinsa a gaban Kotun Tarayya mai sauraron koke-koken zaɓe.

Ƙungiyar ta kuma yi godiya a madadin uban ƙungiyar 10-10 Initiatives Turakin Adamawa Aliyu Atiku Abubakar, bisa ga irin addu’o’in fatan samun nasara da ýan Nijeriya suka riƙa yi wa Atiku Abubakar a lokacin azumin Ramadan da ya gabata cikin sallolin dare da lokutan tafsirai.

“Muna sane da irin ɗimbin goyon bayan da aka riƙa bai wa jagoran mu Atiku Abubakar, da addu’o’in samun nasara da ake cigaba da yi a kowanne mataki, don ya samu nasara a kotun sauraron koke-koken zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

“Muna da ƙwarin gwiwar cewa kotu za ta yi adalci, saboda yadda muka yi imani da ɓangaren shari’a a matsayin maƙurar kare haƙƙokin ýan ƙasa da kare martabar dimukraɗiyya, kuma babu shakka nan ba da daɗewa ba kotu za ta tabbatar wa da jagoran mu Atiku Abubakar nasarar da ya samu.” A cewar ƙungiyar.

Kungiyar 10-10 Initiatives ta sake tunatar da kotu muhimmancin yin adalci da kuma yanke hukunci a cikin wa’adin da dokar zaɓe ta bayar, ba tare da jinkiri ko jan ƙafa ba.

A yayin da ƙungiyar ke taya al’ummar musulmi murna da kammala azumin watan Ramadan da bukukuwan sallar Eid el-Fitr da aka gudanar, ta kuma ga hankalin Nijeriya da dukkan magoya bayan Jam’iyyar PDP da ke faɗin ƙasar nan su ci gaba da zama ýan ƙasa nagari, da yi wa kotu biyayya a kodayaushe.