Month: December 2020

Qanqara- Tun da Garba ya nemi afuwa

Qanqara- Tun da Garba ya nemi afuwa

Tare da Nasiru Adamu El-Hikaya Muhawar yawan xaliban makarantar sakandaren Kankara a jihar Katsina da a ka sace ta zo qarshe tun da an gano yaran ko na ce an samu dukkan yaran har an ma miqa su ga iyayen su. Ba wata baquwar al’ada ba ce a Nijeriya a ba da labari da ya wuce kima ko ya gaza kima musamman hakan ya fi dogara ne ga yadda labarin ya shafi mai ba da shi. Hakanan a lokacin da gwamnati ko jami’an tsaro kan yi qoqarin rage kaifin labari don ta yiwu ya jawo tashin hankali ko zubar da…
Read More
Tsaro: Arewa ta na kan bom, cewar Bafarawa

Tsaro: Arewa ta na kan bom, cewar Bafarawa

Daya daga cikin dattijan Arewa da suke kwana suna tashi cikin tunanin yadda za a shawo kan al’amarin shi ne tsohon Gwamnan Jihar  Sokoto, kuma tsohon xan takarar zama shugaban qasa, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa (Garkuwan Sokoto), wanda har qasida ya tava gabatarwa ga takwarorin sa manyan yankin kan yadda za a yi a tunkari matsalolin Arewa. Editocin jaridar Manhaja sun samu damar zantawa da shi domin ya yi mana qarin bayani kan yadda yake ganin za a tubnkari matsalar. A yayin hirar, Bafarawa ya bayyana dalilan da suka sa ya jagoranci tattara alqaluman asarar da aka yi wa arewacin…
Read More
Rikicin Addini: Salafiyya, Tijjaniya da Kadiriyya

Rikicin Addini: Salafiyya, Tijjaniya da Kadiriyya

Daga FATUHU MUSTAPHA A cikin makon da ya gabata ne, wasu manyan malaman salafiyya, wadanda suka hada da: Sheikh Muhammad bin Abdulwahab da Sheikh Dr. Mansur Sokkoto, suka yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta kama shehin malamin nan na darikar Qadiriya: Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara. Wannan rigima dai ta samo asali ne, tun bayan da shi sheikh Abduljabbar ya fara wani tafsiri da ya kira Jauful Faraa. Tafsirin da mafiya akasarin malaman darikar ta Salafiya ke ganin ya saba qa’ida, ya na kuma wuce gona da iri. Wannan rigingimu dai ba yau aka fara fama da su, a…
Read More
Ni ba Rahama Sadau ba ce- Teema Makamashi

Ni ba Rahama Sadau ba ce- Teema Makamashi

Daya daga cikin fitattun jarumai a cikin masana’antar finafinai ta Kannywood FATIMA ISAH MUHAMMAD wadda aka fi sani da Teemah Makamashi, ta bayyana harkar fim a matsayin wata harkar da ta yi mata rana, domin kuwa kamar yadda ta bayyana wa wakilin mu a lokacin da ya tattaunawa da ita dangane matsayin harkar fim a gare ta. Haka kuma jarumar ta yi tsokaci game da dambarwar Kannywood na Rahama Sadau. Ga yadda hirar ta kasance tare da wakilin mu ALIYU ASKIRA: “Harkar fim ta yi mini rana, saboda ita ta yi mini wando har da riga da bargon da na…
Read More
Balarabe Musa: Gaba ta wuce…

Balarabe Musa: Gaba ta wuce…

Daga Ibrahim Sheme Alhaji Abdulqadir Balarabe Musa mutum ne “wani iri”. Ba a saba ganin irin sa ba. Mutum ne wanda idan an yi Yamma sai ya yi Gabas, idan kuma an yi Kudu shi sai ya yi Arewa. Wasu na kallon sa a matsayin murdadde, ba a yi tanqwasa shi a tattaunawar siyasa; wasu kuma na yi masa kallon mai sauqin kai, mai rungumar talakawa.Ko ma ta wace fuska mutum ya kalle shi, babu wanda zai ce maka ba nagartacce ba ne. Hatta mutanen da ya rayu ya na adawa da manufofin su sun yi ittifaqi da cewa ‘Bala…
Read More
BABU ABIN DA ZAI CIKA SAI DA MACE A CIKI

BABU ABIN DA ZAI CIKA SAI DA MACE A CIKI

HAJIYA HALIMA IDRIS ita ce Mai Taimaka wa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i, a fannin Fikira da Qirqira. Ta yi fice ta fuskoki da dama tun gabanin muqamin ta, musamman wajen kishin Arewa da son cigaban mata da matasa. A wannan hirar da wakiliyar manhaja, AYSHA ASAS, ta  yi da Halima Idris, ta bayyana abubuwa da dama da suka haxa da ayyukan ta  a gwamnati da kuma fannin kwalliya. Ga yadda hirar ta kasance: Kin yi fice a harkokin cigaban matasa da suka shafi fikira da qirqira. Me ya ba ki wannan sha’awar? Gaskiya ba zan iya ce…
Read More
Babban buri na kafin in bar duniya… – Aunty Bilkisu Funtua

Babban buri na kafin in bar duniya… – Aunty Bilkisu Funtua

Daga Aysha Asas Wadanda suka dade da fara karance-karancen littattafan Adabin Kasuwar Kano tun wuraren 1993 ba shakka zan iya cewa sun sha cin karo da littattafan Hajiya Bilkisu Salisu Ahmed Funtua, wadda ake kira Aunty Bilki Funtua, domin ta kasance a sahun farko kuma tauraruwar da littattafanta ke ja a wancan lokacin. Saboda haka a tashin farko muka samu nasarar shigo muku da ita cikin wannan fili don jin wace ce ita, mene ne kuma burinta a halin yanzu sakamakon rashin jin duriyar littattafan ta a kasuwa na dogon lokaci. Ga dai yadda hirar tamu ta kasance: Masu karatu…
Read More
Tsaro: Arewa ta na kan bom, cewar Bafarawa

Tsaro: Arewa ta na kan bom, cewar Bafarawa

Rashin tsaro na daga cikin manyan matsalolin da suka addabi arewacin Najeriya a yau. Abin ya kasance har kusan kowa ya sadaqar, an kasa kamo bakin zaren. A yayin da shugabannin yankin suke ta laluben yadda za a magance matsalar, da yawa kuma sun naxe hannu, sun haqura. Shin menene abin yi? Daya daga cikin dattijan Arewa da suke kwana suna tashi cikin tunanin yadda za a shawo kan al’amarin shi ne tsohon Gwamnan Jihar  Sokoto, kuma tsohon xan takarar zama shugaban qasa, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa (Garkuwan Sokoto), wanda har qasida ya tava gabatarwa ga takwarorin sa manyan yankin…
Read More
Dakin da babu mai iya zaman minti 45 cikinsa

Dakin da babu mai iya zaman minti 45 cikinsa

Daga Umar Mohammed Gombe a Abuja Duk da cewa kusan kowane dan Adam yana buqatar wurin da babu hayaniya don debe kewa ko samun hutu ko nishadi, amma labarin ya kan sauya da zarar mutum ya shiga cikin wani daki, wanda aka yi ittifaqin ya fi kowane daki shiru a Duniya. Dakin mafi ban al'ajabi da ake masa laqabi da 'Anechoic Chamber' ya kasance ne a birnin Minnesota na Qasar Amurka, wanda wani attajiri Steven Orfield ya gina don aiwatar da gwaje-gwajen fasahar software. Jaridar Daily Mail ta Amurka, ta ruwaito cewa tsananin shirun dakin ya kai miqdarin maganadisun ma'aunin…
Read More
Dambe: Buhari ya taya Anthony Joshua murna kan nasarar buge Pulev

Dambe: Buhari ya taya Anthony Joshua murna kan nasarar buge Pulev

Daga ABBA MUHAMMAD Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna farin cikin sa da nasarar da dan damben Nijeriya, Anthony Joshua, ya samu a kan Kubrat Pulev a fafatawar da suka yi a daren jiya Asabar. A sanarwar da ya fitar ta hannun kakakin sa, Femi Adesina, Buhari ya ce Joshua ya bai wa masoya dambe a duniya da ma Nijeriya farin ciki sosai. Shugaban ya ce ya tuna da haduwar da ya yi da Joshua a Ingila, inda ya bayyana shi a matsayin mai saukin kai kuma wanda ya samu tarbiyya, ya ce zai yi nasara sosai a rayuwar sa.…
Read More