12
Dec
Daga Umar M. Gombe Kotun Koli na Amurka ta kawo karshen dogon takaddamar da ya dauki lokaci ana yi game da zaben shugaban kasa a kasar tun a watan Nuwamba, inda ta tabbatar wa dan takarar shugaban kasa na Democrat Joe Biden nasara. A cikin hukuncin da ta yi ba ranar Juma'a, kotun kolin ta kori karar da Shugaba Donald Trump ya shigar game da zargin tafka magudin zabe da aka yi a Pennsylvania da kuma jihohi uku na kasar. Jihohin hudun sun gabatar da shaidu gaban kotun, inda kuma suka bukaci alkalan kotun da su yi watsi da karar,…