31
Jan
Daga UMAR M. GOMBE Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta yi kira ga gwamnan jihar Bello Matawalle, da ya yi amfani da kuɗaɗen fansho Naira miliyan 500 da ke ɓoye a banki an rasa mai su wajen biyan ma'aikatan gwamnatin jihar da suka yi murabus haƙƙoƙinsu. Kazalika, majalisar ta buƙaci Gwamnan da ya nemi ganawa da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari'a, da kuma Babban Daraktan Hukumar Fansho ta Ƙasa domin tattauna yadda za a yi a biya ma'aikatan gwamnati a jihar abin da suka tara a can baya. A cewar Majalisar, "Wannan na daga cikin matsayar da ta cim…