26
Feb
Daga FATUHU MUSTAPHA Babu takamaiman ko wacce shekara aka haifi Ɗanwaire, sai dai an bayyana cewa asalin sunan sa Muhammadu. Iyayen sa da alama dai Fulani ne, kuma asalain sa shi da mutumin Kano ne. an haife shi a garin Waire da ke ƙasar Bichi a yanzu. Babu kuma wani cikakken bayani akan ko wane irin nau’in Fulani ne. A taƙaice dai, asali da tasowar Ɗanwaire abu ne da har yau masana basu samu wani cikakken bayani a ka ba. Amma dai an fara jin ɗuriyar Ɗanwaire ne a zamanin sarkin Kano Bello1882 – 1893. Hakan na nuni da cewa…