Month: March 2021

Shugaba Ramaphosa ya haramta sayar da giya lokacin Easter a ƙasarsa

Shugaba Ramaphosa ya haramta sayar da giya lokacin Easter a ƙasarsa

Daga WAKILINMU Shugaban Ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya ɗauki matakin haramta sayar da giya na kwanaki huɗu lokacin bikin Easter domin daƙile yaɗuwar cutar korona, inji RFI. Da yake jawabi ga al’ummar ƙasarsa, Shugaba Ramaohosa ya ce sun gano cewar mutanen da suka kwankwaɗi giya na aikata laifuffukan da ba su dace ba waɗanda ke yaɗa cutar korona. Don haka ya ce daga ranar juma’a zuwa Litinin masu zuwa, ba za a sayar wa mutane giyar su kai gida ba. Amma za a bar ta ga masu sha a gidajen abinci da mashaya. Mutane sama da miliyan ɗaya…
Read More
Balaguron Buhari: ‘Ba sai Buhari ya miƙa wa Osinbajo ragamar mulki ba’, Fadar Shugaban Ƙasa

Balaguron Buhari: ‘Ba sai Buhari ya miƙa wa Osinbajo ragamar mulki ba’, Fadar Shugaban Ƙasa

Daga FATUHU MUSTAPHA Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa ba lallai ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa ragamar mulki ga mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ba, don ya tafi dubar lafiyarsa a ƙetare. Mai magana da yawun Shugaba Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana haka yayin wani shiri da aka yi da shi a tashar Channels a Talatar da ta gabata. Garba Shehu ya ce Shugaba Buhari bai saɓa wata doka ba na rashin miƙa wa mataimakinsa ragamar mulkin ƙasa alhalin ya bar ƙasa na wasu 'yan kwanaki. Yana mai cewa, "Shugaba Buhari zai ci gaba da gudanar da harkokinsa…
Read More
Gwamnati ta bada hutun kwana biyu albarkacin Bikin Easter

Gwamnati ta bada hutun kwana biyu albarkacin Bikin Easter

Daga FATUHU MUSTAPHA Gwamnatin Tarayya ta bayyana Juma'a, 2 da Litinin 5 ga watan Afrilu, 2021 a matsayin ranakun hutun gama-gari albarkacin Bikin Easter na bana. Ministan Cikin Gida, Ogbeni Rauf Adesoji Aregbesola ne ya sanar da haka a madadin Gwamnatin Tarayya a Abuja. Tare da yin kira ga ɗaukacin al'ummar Kirista da su rungumi ɗabi'ar zaman lafiya, son juna da yafiya kamar yadda Annabi Isa (AS) ya karantar. Haka nan, Ministan ya buƙaci Kirista da su yi amfani da wannan dama ta Bikin Easter wajen yi wa ƙasa addu'ar zaman lafiya ga Nijeriya da kuma samun cigaba mai ɗorewa.…
Read More
Ondo: ‘Yanwasan Sunshine Stars sun yi zanga-zanga saboda rashin biyan albashi

Ondo: ‘Yanwasan Sunshine Stars sun yi zanga-zanga saboda rashin biyan albashi

Daga UMAR M. GOMBE 'Yanwasa da jami'an Ƙungiyar Ƙwallon Kafa ta Sunshine Stars a Jihar Ondo, sun gudanar da zanga-zanga domin nuna rashin jin daɗinsu kan abin da suka kira da rashin kulawa daga ɓangaren Gwamnatin Jihar. Zanga-zangar wadda aka gudanar a birnin Akure ta yi sanadiyar haifar da tsaiko ga harkokin kasuwanci a yankin. Masu zanga-zangar sun yi tattaki ne daga babban filin wasannin motsa jiki zuwa fadar gwamnatin jihar ɗauke da kwalaye masu dauke da saƙonni daban-daban don nuna damuwarsu. Waɗanda lamarin ya shafa sun ce ba su samu albashinsu ba na tsawon wata shida haɗa da sauran…
Read More
Neja: PDP ta dakatar da Babangida Aliyu bisa zargin yi wa jam’iyya zagon-ƙasa

Neja: PDP ta dakatar da Babangida Aliyu bisa zargin yi wa jam’iyya zagon-ƙasa

Daga AISHA ASAS Jam'iyar PDP a Jihar Neja ta bayyana dakatar da Tsohon Gwamnan Jihar Neja, Dakta Mu'azu Babangida Aliyu. PDP ta Ƙaramar Hukumar Chanchaga ta dagatar da Aliyu ne bisa wasu zarge-zarge a kansa ciki har da haifar da rashin jituwa a tsakanin shugabannin jam'iyyar. Kazalika, an zargi Tsohon Gwamnan da yi wa jam'iyya zagon-ƙasa, sai batun rashin martaba faɗar Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai, wanda ya buƙaci a haɗu a gudanar da babban taron jam'iyya na jiha. Haka nan, akwai zargin cewa Dr Mu'azu Babangida Aliyu ya tallafa wa APC da kuɗi Naira milyan N450 yayin zaɓen…
Read More
Filato: Gobara ta yi ta’asa a kasuwar doya a Qu’an Pan

Filato: Gobara ta yi ta’asa a kasuwar doya a Qu’an Pan

Daga WAKILINMU An samu aukuwar mummunar gobara a kasuwar doya ta Namu ta Tsakiya da ke yankin Ƙaramar Hukumar Qu'an Pan, Jihar Filato. Manhaja ta kalto cewa gobarar ta auku ne da daddare a Lahadin da ta gabata inda ta lalata tarin doya da sauran kayayyakin abincin na muƙudan kuɗaɗe. Sai dai ya zuwa haɗa wannan labari, jaridar Daily Nigerian ta ce ba a kai ga gano sababin faruwar gobarar ba. Bayanai daga yankin sun nuna sama da manona 100 ne ibtila'in gobarar ya shafa. Tare da yin kira ga gwamnati a matakai daban-daban da su tallafa wa waɗanda lamarin…
Read More
NAFDAC ta gargaɗi ‘yan Nijeriya kan amfani da jabun shayi

NAFDAC ta gargaɗi ‘yan Nijeriya kan amfani da jabun shayi

Daga WAKILINMU Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC), ta yi jan hankali ga 'yan Najeriya game da wani jabun shayi da ake sayarwa wanda aka ce yana maganin ciwon sukari. Hukumar ta gargaɗi 'yan nijeriya da su guji yin amfani da 'insulin tea' wanda ko rajista bai da shi balle kuma ingancin warkar da wata cuta. Shugabar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta yi wannan gargaɗi a wata sanarwar manema labarai da ta fitar a Lahadin da ta gabata a Abuja. Adeyeye ta buƙaci duk inda aka ga ana sayar da wannan shayi na 'insulin tea' a gaggauta…
Read More
Rashin aiki ga matasa ne silar matsalar tsaron Nijeriya, cewar Atiku

Rashin aiki ga matasa ne silar matsalar tsaron Nijeriya, cewar Atiku

Daga FATUHU MUSTAPH Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya danganta matsalar tsaron Nijeriya da rashin aikin yi ga matasa, inji wata sanarwa da Waziri Adamawa ya fitar a Lahadin da ta gabata. Atiku ya ce bai taɓa jin wata damuwa ba da faɗin abin da shi ne daidai. Yana mai cewa duba da rahoton da Bloomberg Business ta fitar a Asabar da ta gabata, cewa Nijeriya za ta zama ƙasar da ta fi kowace yawan marasa aiki a faɗin duniya inda yanzu adadin narasa aikin ya kai kashi 33 cikin 100. "Wai yaya aka yi Nijeriya ta kai…
Read More