Month: March 2021

Nijeriya ta samu ƙarin mutum 240 da suka harbu da cutar korona

Nijeriya ta samu ƙarin mutum 240 da suka harbu da cutar korona

Daga WAKILINMU An bada sanarwar cewa Nijetiya ta samu ƙarin wasu mutum 240 da suka kamu da cutar korona a 'yan sa'o'in da suka gabata. Cibiyar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ce ta bada sanarwar haka da daddare a Lahadin da ta gabata, ta shafinta na twita. Ƙarin da NCDC ta ce an samu ya shafi wasu jihohi ne su 13 kamar haka: Anambra 85, Lagos 82, Osun 17, Ogun 10, Kwara 9, FCT 8, Kano 7, Abia 6, Ekiti5, Borno 4, Edo 2, Bayelsa 2, Kaduna 2 da kuma Rivers 1. Cibiyar ta ce katafariyar cibiyar bada…
Read More
Minista Bello ya ƙaddamar da shirin kiyaye dokokin hanyoyi a Abuja

Minista Bello ya ƙaddamar da shirin kiyaye dokokin hanyoyi a Abuja

Daga AISHA ASAS Ministan Abuja Malam Muhammad Musa Bello, ya ƙaddamar da shirin yaƙi da karya dokokin hanya a birnin Abuja a matsayin wani mataki na tabbatar da jama'a na kiyaye dokokin hanya yadda ya kamata a cikin birnin. Ƙaddamar da shirin ya auku ne a ƙarshen makon da ya gabata a Abuja. A lokacin da yake jawabi a wajen taron ƙaddamarwar, Bello ya tunatar da mazauna Abuja cewa dukkanin ƙa'idoji da alamomin da aka sanya a hanyoyi, an yi hakan ne da nufin kare rayukan masu amfani da hanyoyin da kuma hana cunkoso. Yana mai cewa, duba da yadda…
Read More
Hukumar Zaɓe za ta yi wa ma’aikatan ta bita kan aikin faɗakarwa

Hukumar Zaɓe za ta yi wa ma’aikatan ta bita kan aikin faɗakarwa

Daga FATUHU MUSTAPHA Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za ta shirya wata bita ta musamman domin wayar da kan ma'aikatan ta na sashen faɗakar da masu zaɓe da ke hedikwatar ta da kuma jihohi. Wata sanarwa da ta fito daga hukumar a ranar Asabar ta ce bitar, mai taken "Faɗakar da Mai Faɗakarwa", wato "Train-the- Trainers (ToT)", an kasa ta zuwa gida biyu saboda matsalar annobar korona (COVID-19) da ake fama da ita. Kashin farko za a yi bitar ga shugabannin sashen faɗakar da masu zaɓe (HODs VEP) da ke jihohin Kudu da kuma waɗanda su ke…
Read More