Month: April 2021

Akwai bambanci ƙwarai tsakanin rubutun zube da na jarida – Mairo Muhammad Mudi

Akwai bambanci ƙwarai tsakanin rubutun zube da na jarida – Mairo Muhammad Mudi

*Ba na zayyana labari irin na abinda ake cewa ‘mijin novel'- Mairo Mudi Daga AISHA ASASSanannen abu ne marubuta sun karkasu daban-daban, inda za ka samu wani ya fi ƙwarewa a rubutun waƙe, ko zube ko kuma wasan kwaikwayo da sauran su, duk da haka akwai wasu tsiraru daga cikin marubuta da aka ba su baiwar shiga kowane ɓangare na Adabi su taka rawar da za a yaba masu. Irin waɗannan marubuta dai su na da karanci domin ba kasafai ake samun su ba. Waɗannan marubuta sun kasance gwanaye a kowane ɓangare na rubutu har a kasa gane wane fage…
Read More
Me ya sa soyayya ke mutuwa bayan Aure?

Me ya sa soyayya ke mutuwa bayan Aure?

Daga AMINA YUSUF ALI Kamar yadda muka sani ko muke iya gani, yawancin aurarrakin yanzu ana dasa su ne bisa soyayya. Wannan abu haka yake musamman a al'ummar Hausa. Da shuɗewar zamani da ilimi har ma da wayewa sun sa an kusa ma a manta a ana auren dole. Amma abu mafi mamaki shi ne, bayan an yi auren soyayyar wacce kamar a haɗiye juna. Sai kuma wasu abubuwa na rashin jituwa su vullo, a rasa ma gane kan zaman nasu. A haka idan ba a kai zuciya nesa ba, sai rabuwa. Ko kuma idan ba a rabun ba, a…
Read More
Ina mafita ga matsalolin Arewa?

Ina mafita ga matsalolin Arewa?

Daga AMINU ƊANKADUNA AMANAWA Arewa yanki ne daga cikin yankunan dake akwai a dunkulalliyar kasa da turawan mulkin mallaka suka hade yankunan kudu da Arewa waje daya da yanzu muke a ciki da kuma tinkaho da ita ta Nijeriya. Duk da yake ko a arewar ta kasu a yankuna daban-daban, kama daga arewa maso gabas, yamma, dama tsakkiya, yankin na fuskantar kalubalai da tarin matsalolin dake kokarin mayar da yankin saniyar ware. Matsalolin da suka tashi daga talauci da kusan ke akwai a lunguna da sako na jihohi, zuwa na tsaro da ya zama ruwan dare, garkuwa da mutane domin…
Read More
Inuwa Ibrahim Waya da tsatsonsa a mahangar tarihi: Kaza da tone-tone?

Inuwa Ibrahim Waya da tsatsonsa a mahangar tarihi: Kaza da tone-tone?

Daga KWAMRED IBRAHIM ABDU ZANGO Siyasa wata aba ce wacce ake yin ta domin kyautata wa al’umma a kowacce ƙasar duniya, wacce ake yin zaɓe, domin mulki irin na zamani. Gaskiya kamar yadda tarihi ya nuna an fara salon wannan mulki tun tale-tale, kususan a can wata ƙasa wacce ita ce farkon bayyanar Turawan duniya. Haka dai abin yake kuma a wancan duniyar Turawa wacce ita ce ta buɗewa dukkan duniya harkar dimukraɗiyya, wacce yanzu ta haɗe duniya kaf ɗinta. Duk da cewa waccan ƙasa ita ce farko, amma mun karanta tarihinta a makaranta wadda har rumawa suka rungume ta…
Read More
Tsaro: Gwamnonin Arewa na da rawar takawa

Tsaro: Gwamnonin Arewa na da rawar takawa

Duk da matsayin da jihohin yankin Arewacin Nijeriya suka samu kawunan su a cikin shekaru 16 da su ka shuɗe har zuwa yanzu da gwamnatin APC ke mulkin ƙasar, alamuran yankin suka shiga taɓarɓarewa, harkar tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma ya kau, kusan kowane ƙauye su na fama da ruɗani masu garkuwa da mutane, don amsar kuɗin fansa, su na fama da hare-hare da rigingimun makiyaya. Gwamnonin da haƙƙin hakan kuma ya rataya a wuyan su ba su taɓuka ba, don ɗaukar wani mataki, walau na gaggawa ko wanda aka tsara na musamman, don magancewa. Haka nan su na ji,…
Read More
Wata Guguwa

Wata Guguwa

Daga AMINA HASSAN ABDULSALAM Bayan fargaba da asarar rayuka da dunkiyoyi da annobar kwarona ta haddasa, rayuwa ta fara dawowa daidai a wasu wurare da dama, harkoki sun fara komawa kamar yadda aka san su. Farkon ɓullar wannan cuta mutane da dama ba su ɗau abin da muhimmanci ba, tunanin kowa shine cutar za ta tsaya ne a iyakar inda ta ɓulla kamar yadda aka saba, abu kamar wasa sai ga ta ta game duniya gabaɗaya ta buwayi duniya har ta illata tattalin arzuƙin mutane da ƙasashe da dama musamman ƙasashe masu tasowa da kuma talakawanta. Har yanzu ba wai…
Read More
Za mu tsige Buhari muddin magance matsalar tsaro ya faskara – Hon Bagos

Za mu tsige Buhari muddin magance matsalar tsaro ya faskara – Hon Bagos

Daga AISHA ASAS Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar shiyyar Jos ta Kudu da Jos ta Gabas a Majisar Wakilai ta Ƙasa, Dachung Bagos, ya ce majalisa za ta ɗauki matakin tsige Shugaba Muhammadu Buhari muddin Majalisar Zartarwa ta Kasa ta kasa kawo ƙarshen matsalolin tsaron da suka addabi ƙasa. Ɗan majalisar ya yi wannan furuci ne yayin wani shiri da aka yi da shi a wannan Alhamis ɗin a tashar talabijin ta Channels. Idan dai za a iya tunawa, ko Larabar da ta gabata sai da majalisar ta kafa wani kwamiti na mutum 40 tare da ɗora masa aikin binciko…
Read More
Jami’ar Edusoko mafita ce ga ɗaliban Neja masu neman gurbin karatu – Gwamna Bello

Jami’ar Edusoko mafita ce ga ɗaliban Neja masu neman gurbin karatu – Gwamna Bello

Daga BASHIR ISAH Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja, ya ce kafa Jami'ar Edusoko zai taimaka wajen magance ƙalubalen samun gurbin karatu da ake fama da shi a jihar Neja. Gwaman ya bayyana haka ne sa'ilin da ya karɓi baƙuncin Kwamitin Amintattu na Jami'ar Edusoko ƙarkashin jagorancin Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, a fadar gwamnatin jihar da ke Minna. Ya ce akwai ɗimbin ɗalibai a jihar Neja da ke neman gurbin karatu a jami'a, yana mai cewa zuwan Jami'ar Edusoko zai zama mafita ga ɗaliban. Baya ga yaba wa Etsu Nupe bisa ƙoƙarin samar da wannan jami'a, Gwamna Bello…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta bayyana 3 ga Mayu, ranar hutun ma’aikata

Gwamnatin Tarayya ta bayyana 3 ga Mayu, ranar hutun ma’aikata

Daga WAKILINMU Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin mai zuwa, 3 ga Mayu, 2021, a matsayin ranar hutun ma'aikata albarkacin bikin Ranar Ma'aikata ta Duniya na bana. Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Adesoji Aregbesola, shi ne wanda ya sanar da hakan a madadin Gwamnantin Tarayya, inda ya yi amfani da wannan dama wajen taya ma'aikata a Nijeriya murnar zagayowar wannan rana. Ministan ya jinjina wa ɗaukacin ma'aikata bisa irin haƙuri da juriya da fahimtar da suke nunawa haɗa da goyon bayan da suke bai wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a ƙoƙarinta da take yi na ciyar da ƙasa gaba da…
Read More
An cafke ‘yan fashi 6 ɗauke da shanu 183 da kuɗi dubu N268 a Oyo

An cafke ‘yan fashi 6 ɗauke da shanu 183 da kuɗi dubu N268 a Oyo

Daga AISHA ASAS Rundunar tsaro ta musamman a jihar Oyo mai ƙunshe da 'yan bangan OPC da Amotekun da VGN, ta cafke wasu mutun shida da ake zargin 'yan fashin daji ne a safiyar Alhamis da ta gabata ɗauke da shanu 183 a yankin ƙaramar hukumar Kajola ta jihar. A cewar Kwamandan Amotekun na jihar Oyo, Col Olayinka Olayanju (mai murabus), ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a hanyar Okeho zuwa Ilua da kuma hanyar Okeho zuwa Iseyin da misalin ƙarfe 4 na asuba na wannan rana. Kwamandan ya ce sun kama ɓarayin ne bayan ɗauki ba daɗin…
Read More