Month: May 2021

Sau 41 aka kai wa ofisoshin INEC hari cikin shekara 2 — Yakubu

Sau 41 aka kai wa ofisoshin INEC hari cikin shekara 2 — Yakubu

Daga AISHA ASAS Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa an kai wa kadarorin hukumar hari har sau 41 a sassa daban-daban na ƙasar nan a cikin shekara biyu da ta gabata. Yakubu ya faɗi haka ne a taron gaggawa da hukumar ta yi da hukumomin tsaro ƙarƙashin Kwamitin Tuntuɓa kan Tsaron Harkar Zaɓe, wato 'Inter-agency Consultative Committee on Election Security' (ICCES). Yakubu ya ce ya kamata daga yanzu a ɗau hare-haren da ake kai wa kadarorin hukumar a matsayin babban abin damuwa ga ƙasa baki ɗaya. Ya ce, “Ba shakka, makwannin da su ka gabata sun…
Read More
Da ɗumi-ɗuminsa: An zaɓi sababbin shugabannin ƙungiyar ANA a Kano

Da ɗumi-ɗuminsa: An zaɓi sababbin shugabannin ƙungiyar ANA a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Kungiyar Marubuta ta Ƙasa reshen jihar Kano, wato Association of Nigeria Author's (ANA) ta zaɓi sabbin shugabanni. Zaɓen ya gudana ne a ɗakin karatu na murtala Muhammad da ke kan Titin Ahmadu Bello da ke Kano. Dr. Maryam Ali Ali ce ta Jagoranci gudanar da zaɓen, waɗanda aka zaɓa sun hada da: Tjjani Muhammad Musa a matsayin shugaba, sai mataimakiyarsa Maimuna Idris Beli, da Mazhun Idris Ya'u a matsayin sakatare. Haka kuma an zaɓi Danladi Z. Haruna a matsayin Ma'aji da sakataren kuɗi Abdullahi Lawan Kangala. Sai jam'in walwala Hausa, da Abdullahi Muhammad a matsayin…
Read More
Ƙungiyar marubutan Arewa ta yi taro don inganta tafiyarta

Ƙungiyar marubutan Arewa ta yi taro don inganta tafiyarta

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Ƙungiyar marubutan Arewa mai suna Authors Forum m, ta yi zaman tattaunawa dangane da yadda za a shirya taron gani da ido karo na farko tare dukkanin mambobinta da ke faɗin ƙasar Nijeriya. Wannan ƙungiya mai farin jini ta marubutan Arewa, ta shirya zama na musamman domin Tattauna muhimman batutuwa a ciki har da ƙirƙiro taron gani da ido don sada zumunci tsakanin marubuta da kuma ƙara wa juna sani a karo na farko. Shi dai wannan zama an yi shi ne a kano inda uwar ƙungiyar ta fito wacce take da rassa a jahohi…
Read More
Ɗaliban Greenfield 14 sun samu ‘yanci

Ɗaliban Greenfield 14 sun samu ‘yanci

An sako ɗalibai 14 na Jami’ar Greenfield ta Jihar Kaduna da ’yan bindiga suka sace daga ɗakunansu na kwana tun a watan Afrilun da ya gabata. Bayanai sun nuna an sako aɗaliban ne a ranar Asabar bayan biyan kuɗin fansar da ba a fayyace ba. Mai Magana da yawun jami’ar, Kator Yengeh, ya tabbatar wa manema labarai da batun sako ɗaliban, tare da cewa nan gaba kaɗan Hukumar Gudanarwar Jami'ar za ta yi ƙarin haske kan lamarin.
Read More
An yi kiciɓis tsakanin Atiku da Tinubu a filin jirgi

An yi kiciɓis tsakanin Atiku da Tinubu a filin jirgi

Daga BASHIR ISAH Jigo a jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya tarbi Tsohon Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar a filin jirgi yayin da ya dawo daga hutun da ya tafi ƙasar waje. Atiku Abubakar ya isa babban filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ne da daddare a Juma'ar da ta gabata. Atiku ya bar Nijeriya na tsawon lokaci inda ya tafi hutu a ƙetare. A matsayinsa na ɗan hamayya, Atiku ba ya sanya wajen faɗin albarkacin bakinsa dangane da batutuwan da suka shafi ƙasa. Sai dai babu wani ƙarin bayani kan ko haɗuwar jigogin biyu shiryayyen allamari ne ko…
Read More
Bagudu ya kama hanyar hana aukuwar haɗurran jiragen ruwa

Bagudu ya kama hanyar hana aukuwar haɗurran jiragen ruwa

Daga AISHA ASAS A matsayin wani mataki na hana aukuwar haɗurran jiragen ruwa a jihar Kebbi da kan yi sanadiyyar hasarar rayuka da dukiyo, gwamnan jihar Atiku Bagudu, ya ce za su duba su yi wa dokokin amfani da kan ruwa na jihar kwaskwarima. Bagudu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a ranar Asabar ta hannun mai bai wa gwamnan shawara kan sha'anin yaɗa labarai, Malam Yahaya Sarki, a Birnin Kebbi. Sanarwar ta nuna Bagudu ya yi wannan bayani ne sa'ilin da ya kai ziyarar ta'aziyya ga Sarkin Yauri, Dr Muhammad Zayyanu a…
Read More
Almudahana: EFCC ta ƙwato sarƙoƙi na bilyan N14.4 a hannun Diezani

Almudahana: EFCC ta ƙwato sarƙoƙi na bilyan N14.4 a hannun Diezani

Daga UMAR M. GOMBE Shugaban Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya bada bayanin cewa kimar kayan kwalliyar da aka ƙwato daga hannun tsohuwar Ministar Makamashin Fetur, Diezani Alison-Madueke, ya kai Naira bilyan N14.4. Shugaban na EFCC ya bayyana hakan ne a Juma'ar da ta gabata a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin Majalisar Wakilai mai bincike kan kayayyakin sata da aka ƙwato, in ji tashar Channels. Bawa ya ce, "Kayan kwalliyar da aka ƙwato a hannun tsohuwar ministar, tsadarsu ya kai Naira biliyan N14.4 kamar yadda hukumomi suka bayyana…
Read More