28
May
Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano A 'yan kwanakin nan babu abin da ya fi ɗaukar hankalin mutane kamar labarin rabuwar auren Sani Danja da Matarsa Mansurah Isah. Labarin dai ya fara ne tun daga ranar Larabar da ta gabata, in da ita Mansurah ta bada sanarwa a shafinta na Instagram cewa ba su tare da mijinta Sani Danja. To sai dai ba ta yi wani ƙarin bayani ba, sannan kuma bayan ɗan wani lokaci da saka labarin sai ta yi sauri da goge shi. Bayan wannan kuma ba ta ƙara cewa komai ba a kan lamarin. Wakilinmu ya yi ƙoƙarin…