2023: Ƙauran Bauchi ya nemi a shure baƙin haure a zaɓen gwamna

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Bisa hangen gabatowar zaɓen gama-gari na ƙasa, Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya gargaɗi masu kaɗa ƙuri’a da kada su zaɓi baƙin ‘yan takara, musamman ma waɗanda suka shigo daga ƙasashen ƙetare na maƙwabta.

Gwamnan, ya yi wannan gargaɗi ne yayin da yake ganawa da shugabannin gundumomi na jam’iyyar PDP na ƙaramar hukumar ta Alkaleri, wacce ta kasance gida a gare shi, a wani taron ganawa da juna da suka yi a yankin ƙaramar hukumar, a kwanakin baya.

Sanata Bala, wanda shi ke riƙe da sarautar gargajiya ta Ƙauran Bauchi, ya ce dole ne masu kaɗa ƙuri’a su guje wa zaɓen baƙi, musamman ma a zaɓen masu takarar kujerar gwamnan jiha, domin kawar da rashin taɓuka komai akan karagar mulki.

Ya bayyana cewar, zaven ɗan ƙasa nagari zai bayar da dama wa waɗanda aka zava, su gudanar da hulɗoɗin ci gaba da jama’ar su, tare da shawo kan ƙalubaloli da ke addabar yankuna ko al’ummomin su, da zummar cimma burace-buracen rayuwa.

“Ina so na tsananta gargaɗi wa jama’ar Jihar Bauchi kan zaɓen waɗanda ba ‘yan ƙasa ba a zaɓen gama-gari mai gabatowa, musamman baƙin haure da suka ƙetaro daga maqociyar ƙasar Jamhuriyar Kamaru, ‘domin ba za su taɓuka wani abu na ci gaba ba’.

Sanata Bala ya ce, “idan ire-iren waɗannan mutane sun shigo ne saboda gudanar harkokin kasuwanci, a shirye muke da mu karɓe su, amma ba harkokin siyasa ba saboda, kamar yadda ya ce, ‘harkar siyasa lamari ne na waɗanda suka san kimar jama’ar su’.

Gwamnan dai, wataƙila yana yin shaguɓe ne wa tsohon babban hafsan mayaƙan sama, Ambasada Sadiq Abubakar, wanda a halin yanzu yake kaɗa gangar tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar Bauchi a zaɓen shekara ta 2023, wanda kuma ake yi wa ƙagen kakansa ya shigo ne daga ƙasar Kamaru.

Shi dai, Sanata Bala Mohammed, yana kammala wa’adin farko ne na mulkin sa akan karagar kujerar gwamnan jihar Bauchi, wanda alamu suka nuna zai tsaya takarar neman wa’adin mulki na biyu a zaɓen shekara ta 2023 ƙarƙashin tutar jam’iyyar sa ta PDP, kuma ga alama zai fuskanci ɗaya daga cikin tara manema takarar kujerar gwamna a jam’iyyar APC, daga cikin su har da Ambasada Sadiq Abubakar, wanda ake ganin yabyi zarra wa sauran.

Daga nan, sai Gwamna Bala ya yabawa shugabannin gundumomi na jam’iyyar ta PDP dake ƙaramar hukumar Alkaleri, tare da buƙatar kada su gajiya wajen ganin ɗorewa nasarorin jam’iyyar PDP a jihar Bauchi.

Ya kuma yi la’akari da cewar, duk da ɗimbin nasarori da gwamnatin sa ta samu wajen samar da romammakin dimokuraɗiyya wa ɗaukacin al’ummar jihar Bauchi, yana bai wa jama’a tabbacin dagewa a kan wannan aniyya ta cigaba da inganta rayuwar jama’ar jihar.

Shi ma da yake yin jawabi, shugaban jam’iyyar PDP na ƙaramar hukuma ta Alkaleri, Alhaji Babayo Alkaleri, ya jaddada goyon bayan su, tare da haɗin kai wa Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ta yadda kwalliya zabta biyu kuɗin sabulu.