2023: Ƙungiyar Arewa ta buƙaci masu neman shugabanci daga Arewa su zakuɗa gefe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Yayin da yaqin neman zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2023 ke ƙara ƙaratowa a faɗin Nijeriya, qungiyoyin ’yan Arewa a ƙarƙashin inuwar ƙungiyar ‘Arewa Coalition for Rotational Residential’ sun yi kakkausar suka kan masu neman shugabancin ƙasar daga Yankin Arewa, inda suka ce babu adalci a Arewa ta ci gaba da mulkin ƙasar bayan shekaru takwas.

Ƙungiyar ta kuma sha alwashin cewa a zahiri za ta tashi tsaye wajen tunkarar duk ’yan takarar shugaban ƙasa daga yankin Arewa, waɗanda suka kuskura su tsaya takara a ƙarƙashin kowace jam’iyya a lokacin babban zaɓe.

Wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar Abdullahi Biu da sakataren Hamza Malumfashi, ta ce za a yi adalci ga kujerar shugaban ƙasa ta dawo kudu bayan wa’adin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya cika.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “takaddamar siyasar da ta kunno kai a halin yanzu sakamakon kiraye-kirayen miƙa mulki zuwa kudu da gwamnonin Kudu da ƙungiyoyi ke yi ba za a iya kawar da su ba ne kawai, idan duk masu ruwa da tsaki daga Arewa da gwamnoni da jam’iyyun siyasa suka amince da fadar Shugaban ƙasa.”

“Domin zaman lafiya, adalci da gaskiya, fiye da yadda Arewa ta kwashe shekaru takwas tana mulki, ya kamata a yi gaggawar kawar da tunanin yarewa ko da tsayawa takarar shugaban ƙasa.

“Duk waɗanda suka zaɓi fom ɗin tsayawa takara, musamman daga jam’iyyar PDP ya kamata su sauka idan akwai masu bin tafarkin dimokraɗiyya na gaskiya.

“A matsayinmu na gungun ’yan dimokraɗiyya daga jihohin Arewa 19, mun yi imani da ƙa’idar daidaito da adalci a matsayin maganin zaman lafiya; ci gaba kuma, ta haka ƙudurinmu ya goyi bayan miqa mulki ga ’yan uwanmu a yankin kudanci.

“A bisa haka ne muke ba wa dukan jam’iyyun siyasa shawara, musamman manyan jam’iyyu biyu, APC da PDP da su tsayar da ’yan takarar Kudu kaɗai.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *