2023: Ƙungiyar matasa ta bai wa Bala wa’adin ya bayyana aniyarsa ta takarar shugaban ƙasa

Daga UMAR M. GOMBE

Ƙungiyar Shugabannin Matasan Arewa (NYLF) ta bai wa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, wa’adi a kan ya fito ya bayyana amincewarsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam’iyyar da ya ji ya fi gamsuwa da ita ko kuma a manta da batunsa a harkokin siyasa a gaba.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Elliot Afiyo, ya bayyana cewa bincikensu ya gano Gwamna Bala shi ne ɗaya tilo da ya fi cancantar zama shugaban ƙasa na gaba.

Sa’ilin da yake miƙa wa Bala wasiƙar neman ya fito ya bayyana sha’warsa ta tsayawa takarar a babban zauren taro na Fadar Gwamnatin jihar a Larabar da ta gabata, shugaban NYLF, Afoul, ya ce sakamakon bincikensu ya nuna a halin da ake ciki babu wanda ya fi dacewa ya riƙe Nijeriya sai Bala Abdulƙadir.

Ya ci gaba da cewa, “Yayin wani taron shugabannin ƙungiyar na ƙasa da muka gudanar a Gombe, mun yi nazarin mutum 47 a faɗin ƙasa dangane da shugabancin Nijeriya amma sunan Bala Mohammed ne ya zama kan gaba.

A nasa ɓangaren, da yake jawabi kan buƙatar da NYLF ta gabatar masa, Gwamna Bala ya ce, “Ni ne ɗan siyasar da aka fi nema ruwa a jallo da kuma wahalawar a wannan ƙasa ne, tun a 2007 da na kayar da wani gwamna mai barin gado na zama sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu har zuwa lokacin da na zama Ministan Abuja, haka na yi ta fuskantar baƙar adawar siyasa.

“Amma ban bari wannan ya zama matsalata ba, haka na ci gaba da fafutikar abin da na sa gaba. Allah cikin ikonSa sai ga shi yau na zama zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Bauchi. Haƙiƙa Allah Ya yi mana falala ni da iyalina”.

Dangane da kiran da ƙungiyar matasan ta yi masa, Bala Mohammed ya ce, “Yanzu dai ba zan iya ba ku amsa ba, sai na nemi shawarwari a siyasance sannan in fito in bayyana matsayata. Zan dogara ne ga neman zaɓin Allah da kuma shawarwari daga mazaɓata. Ku ba ni mako biyu zuwa uku zan ba ku amsata.