Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Gamayyar Ƙungiyoyin Arewa (CNG), ta caccaki ’ya’yan Ƙungiyar Dattawan Ibo (IECF) da sauran ƙungiyoyin da ke fafutukar ganin an tsayar da shugaban ƙasa a yankin Kudu Maso Gabas, inda suka ce suna tada hankalinsu ta hanyar da ba ta dace ba.
Ƙungiyar ta CNG ta yi zargin cewa, dattawan ƙabilar Ibo sun zama babbar barazana ga tsaro a ƙasar, inda ta ƙara da cewa, gargaɗin da suka yi a baya-bayan nan cewa duk wani yunƙuri na kaucewa shiyyar Kudu Maso Gabas na tsayar da shugaban ƙasa a 2023 zai ruguza kasuwancin Nijeriya.
Don haka ƙungiyar haɗin kan Arewa ta yi kira da a gaggauta kama mambobin ƙungiyar ta IEC a ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Anambra, Cif Chukwuemeka Ezeife, saboda barazana ga al’umma da cibiyoyinta da kuma jama’a.
Kakakin CNG, Abdulazeez Suleiman, a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja, ya kuma caccaki wasu shugabannin ƙabilar Ibo da a cewarsa, ke ƙishirwar samar da shugaban ƙasar Nijeriya mai jiran gado bisa zarginsu da neman yi wa tsarin shari’ar ƙasar zagon ƙasa, ta hanyar matsa lamba a sake su Nnamdi Kanu ba tare da wani sharaɗi ba.
Idan dai za a iya tunawa, an yi ta tafka kura-kurai a siyasance, tarwatsa jama’a musamman yadda wa’adin mulkin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya cika shekaru takwas, wanda ya fito daga yankin Arewa maso Yamma, ya cika.
Sai dai tun daga lokacin da ake ta cece-kuce game da zaɓen shugaban ƙasar Ibo ya yi ƙamari ne da wasu watanni 18 a gudanar da babban zaɓen ƙasar, musamman yadda ƙungiyar ƙoli ta al’adun ƙabilar Ibo, Ohanaeze Ndigbo ta duniya, ta yi daidai da buƙatar ta na neman shugaban ƙasar Ibo a 2023.
Sai dai ƙungiyar ta CNG ta ce, cigaba da kai hare-hare kan wakilai da alamomin Gwamnatin Tarayyar Nijeriya a yankin Kudu maso Gabas ya ƙara dagula fargabar cewa ƙabilar Ibo ba za ta iya ba kuma ba za a taɓa amincewa ta riƙe ƙasar ba, wanda hakan ya sanya suka sake nuna rashin jin daɗinsu ga shugabancin Ibo.
Suleiman ya ce, “gamayyar ƙungiyoyin Arewa (CNG), ta yi nazari a kan abubuwan da suka faru a Nijeriya, musamman a ’yan watannin da suka gabata, lokacin da dimokuraɗiyyarmu, haɗin kan siyasa da tsaron kasa suka shiga tsaka mai wuya, musamman ganin irin tashe-tashen hankula da suka haifar da tarzoma a kusa da wasu muradun al’ummar Ibo.
“An tabbatar da hakan ne daga kalamai da ayyukan shugabannin Ibo kamar yadda tsohon gwamnan jihar Anambra kuma shugaban ƙungiyar tuntuɓa ta dattawan Ibo, Chukwuemeka Ezeife, a lokacin da ya yi barazanar cigaba da kasancewar
“An tabbatar da hakan ne daga kalamai da ayyukan shugabannin Ibo kamar yadda tsohon gwamnan jihar Anambra kuma shugaban ƙungiyar tuntuɓa ta dattawan Ibo, Chukwuemeka Ezeife, a lokacin da ya yi barazanar cigaba da kasancewar Nijeriya a ziyarar jaje da shugabannin Ibo suka kai masa na tunani da sarakunan gargajiya a ranar 5 ga Afrilu, 2022.
“Hakazalika, ƙungiyoyin shugabanni da dattawan Ibo sun shiga tsaka mai wuya wajen ganin an sako Nnamdi Kanu, shugaban ƙungiyar ta’addanci ta IPOB da ke fuskantar shari’a kan laifukan da suka shafi jihar ba tare da wani sharaɗi ba.
“Kamar waɗannan ba su isa ba, ƙungiyar dattawan Ibo ta sake fitar da wata barazana ga tsaron ƙasa a ranar 4 ga Mayu, 2022, cewa duk wani yunƙuri na kuvuta daga shiyyar shugaban ƙasa a 2023 na iya ruguza wanzuwar Nijeriya a matsayinta, kamar yadda rikicin ya ta’azzara, tashe-tashen hankula, buƙatar ‘yan aware da sauransu.
CNG ta lura cewa, masu aikata wannan tashe-tashen hankula na rashin hankali suna cigaba da aiwatar da ajandar halaka da tarzoma baki ɗaya, tare da fatan hakan zai mamaye ɗaukacin ƙasar da kuma sake haifar da yaqin basasa da kashe-kashen jama’a.
“Hakan ya ƙara zurfafa fargabar cewa Ibo ba za su iya ba kuma bai kamata a amince da su da ikon shugaban ƙasa ba kuma ya sake sanya su ƙara nuna rashin jin daɗi ga wanda ake zargin shugaban ƙasar Ibo.
“Abubuwan da suka faru a baya sun sa ba za mu iya yin ko-in-kula ba ko kuma yin shiru a duk lokacin da ake fuskantar irin wannan tada zaune tsaye da kuma dagewa zuwa ga rikicin cikin gida.