2023: Ɗan takarar Gwamnan Nasarawa a PDP ya zaɓi mataimakinsa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Ɗan takarar kujerar Gwamnan Jihar Nasarawa a zaɓen shekarar 2023 a inuwar Jami’iyyar PDP, Honorabul Joseph Ombugadu ya sanar da Alhaji Yahaya Usman Ohinoye a matsayin mataimakinsa a takarar kujerar.

Da yake jawabi wa ɗimbin magoya bayan jam’iyyar da manema labarai jim kaɗan bayan ya sanar da mataimakin nasa, Joseph Ombugadu ya bayyana cewa da shi da ƙungiyar yaƙin neman zaɓensa da sauran shugabannin jam’iyyar a jihar sun ga ya dace ne su zaɓi Alhaji Yahaya Usman Ohinoye don ya mara masa baya a tafiyar idan aka yi la’akari da cancantarsa da kuma ƙwarewarsa musamman a matsayinsa na tsohon ɗan majalisa yake bada gagarumin gudunmawa wajen cigaban jam’iyyar da jihar baki ɗaya, inda ya qara da cewa ba shakka zaɓin nasa zaɓi ne nagari.

Daga nan sai ya buƙaci sabon wanda aka zaɓan ya tabbatar ya yi aiki tuƙuru don cimma nasara a ƙarshe.

Tun farko a jawabin shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Honorabul Francis Orogu ya bayyana cewa kawo yanzu jam’iyyar tana aiki tuquru don tabbatar ta ƙwace ragamar mulkin jihar daga gun APC wacce a cewarsa ta kasa samar wa al’ummar jihar romon dimukuraɗiyya, inda ya yi amfani da damar ya buqaci al’ummar jihar baki ɗaya su zaɓi PDP a zaɓukan dake tafe don a cire musu kitse daga wuta.