Daga AMINA YUSUF ALI
Sunan Muhammad Abacha ya yi vatan dabo a cikin jerin sunayen ‘yan takarar Gwamnan Kano a 2023 da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Nijeriya (INEC) ta saki a ranar Talatar da ta gabata.
Haka zalika, sunan ɗan takarar gwamnan jihar Kano a ƙarƙashin jami’yyar LP, Bashir Ishaq Bashir shi ma ya yi layar zana a dai jadawalin na INEC. Amma sai aka maye gurbin sunansa da sunan wani Abdullahi Mohammed Raji.
Shi kuma Assadiq Wali, sunansa shi ne ya fito a matsayin ɗan takarar na PDP a jihar Kano. Wannan ya sanya ‘yan jam’iyya cikin ruɗani a kan wa za su bi a matsayin ɗan takararsu na gwamna.
Kodayake kuma, idan muka dubi abin ta wani ɓangaren, wannan jerin sunaye da INEC ta saki ya zama raba-gardama wanda zai kawo ƙarshen rikicin cikin gida na jam’iyyar PDP a kan waye ɗan takararta na halas tsakanin Abacha da Sadiq Wali.
Domin kuwa kafin sakin wannan jadawalin, kowanne a cikinsu yana iƙirarin shi ne halstaccen ɗan takarar jam’iyyar.