2023: Adamu ya ƙalubalanci shugabancin APC na Abia ya daidaita al’amuran jam’iyyar a jihar

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya yi kira ga shugabancin jam’iyyar a Jihar Abia da haɗa kan ‘yan jam’iyyar jihar tare da sulhunta taksanin waɗanda suke ganin an saɓa musu.

Adamu ya buƙaci su yi tsayin daka don kai bantensu a zaɓen 2023 maimakon shan kaye kada daga bisani su tattara su koma Abuja.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan kammala taron Kwamitin Gudanarwa na jam’iyyar inda aka kafa kwamitin sulhunta ‘yan jam’iyyar a Abia, Adamu ya ce ba zai lamunci shan kayen jam’iyyar ba.

Ya ce, “Ya gana da shugabannin APC na Abia waɗanda yin sulhun ya shafa. Mun yi taro da dama da Kwamitin Gudanarwa yayin zaɓen fidda gwani.

“Ina fatan abin da muka yi yau, duniya za ta shaida lumana, kuma muna fata wannan ya zama matakin ƙarshe. Ba za mu sake yin wani taron sulhu ba.

“Za mu sakar wa shugabannin APC na Abia ragama kan su kula da sha’anin siyasar Jihar Abia. Abuja ba don Abia ba ne, ku koma gida ku kula da lamarin siyasarku….,” inji Adamu.

A ƙarshe, Adamu ya nusar da ‘yan taron da ma ‘yan APC baki ɗaya buƙatar da ke akwai a haɗa kai a yi aiki tare don iya lashe zaɓe a kowace jiha.