2023: APC ta ƙaddamar da kwamitocin tantance ’yan takara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jam’iyyar APC za ta ƙaddamar da kwamitocin tantance ’yan takarar majalisar wakilai, dattijai da na gwamnoni da ta tantance a yau da ƙarfe 12 na rana.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da Sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sulaiman Argungu ya fitar.

A cewar Argungu, za a ƙaddamar da kwamitin tantancewar ne a Fraser Suites, Abuja.

Ya kuma bayyana cewa, daga nan ne za a fara tantance masu neman kujerar gwamna, majalisar wakilai da kuma ’yan majalisar dattawa.

Argungu ya ce, za a gudanar da tantance ’yan takarar majalisar wakilai a ranar Asabar 14 ga Mayu, 2022 a otel ɗin Zeus Paradise, Abuja da ƙarfe 2 na rana.

Ya bayyana cewa, za a gudanar da tantance masu neman takarar Sanata da Gwamna a ranar 15 ga Mayu, 2022 a Fraser Suites, Abuja ranar Lahadi, da ƙarfe 10 na safe.

Jam’iyyar APC ta tsayar da ranar Juma’a 13 ga watan Mayun 2022 a matsayin ranar da za ta miƙa dukkan fom.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *