2023: APC ta musanta tara kuɗaɗe don bai wa masu kaɗa ƙuri’a

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jam’iyyar APC mai mulki ta musanta wani rahoto da ake yaɗawa cewa, jam’iyyar na shirin tara kusan Naira Tiriliyan 6.5 don sayen ƙuri’u, da bai wa jami’an tsaro cin hanci da kuma Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) don cin zaɓen 2023.

Sai dai jam’iyyar APC ta zargi jam’iyyar PDP da cewa ita ce ke da alhakin wannan jita-jita.

Da ya ke mayar da martani kan zargin ta hanyar wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na ƙasa, Felix Morka ya sanyawa hannu a ranar Litinin a Abuja, ya bayyana takardar da aka fallasa a matsayin wata dabara ta ’yan adawa.

A bisa kuskure, takardar ta yi zargin cewa Jam’iyyarmu ta zaɓi kuɗi naira tiriliyan 6.5 don samar da wasu tsare-tsare da nufin zaburar da al’ummar Nijeriya wajen marawa jam’iyyar da ɗan takararta na Shugaban ƙasa goyon baya a 2023.

Sanarwar ta ce, APC ta mayar da hankali ne wajen isar da rabe-raben dimokuraɗiyya ga ’yan Nijeriya da fatan za su mayar da martani ta hanyar goyon baya da kuma zaɓen ’yan takararmu a zaɓen 2023. Mu jam’iyya ce mai bin doka kuma ba mu da buƙatar shiga duk wata zamba da zaɓe da aka nuna a cikin wannan takarda mara amfani.

Jam’iyya mai mulki ta buƙaci ’yan Nijeriya da su yi watsi da wannan takarda a matsayin farfaganda ce marar tabbas wacce PDP ta ke yaɗawa.