2023: APC ta tsayar da ranakun zaɓen fidda gwanin ’yan takara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Jam’iyyar APC ta tsayar da ranar 30/31 ga watan Mayu a matsayin ranar da ta shirya gudanar da zaɓen fidda gwani na ’yan takarar shugaban ƙasa.

Ta kuma tsayar da ranar 23 ga Mayu don gudanar da zaɓen fidda gwani na ’yan takarar gwamna.

Jam’iyyar, a cikin wata wasiƙa da ta aike wa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), mai kwanan ranar 6 ga watan Afrilu, ta sanar da hukumar zaɓe ranakun da jadawalin zaɓen fidda gwani na fitar da ’yan takara a zaɓen 2023.

Manema labarai sun samu kwafin wasiƙar ne ta hannun Iyiola Omisore, sakataren jam’iyyar APC na ƙasa.

Jam’iyyar ta kuma sanya ranar 11 ga watan Mayu za a gudanar da zaɓukan fidda gwani na ’yan majalisun jihohi, majalisar wakilai za ta gudana ne a ranar 16 ga watan Mayu yayin da gundumomin ‹yan majalisar dattawa za su yi a ranar 18 ga watan Mayu.

“Wannan sanarwa ce ta hukuma, bisa tanadin sashe na 85 na dokar zaɓe ta 2010 da aka yi wa kwaskwarima. Da fatan za a shirya jami’ai don sanya ido kan aikin yadda ya kamata. Yayin da mu ke fatan samun haɗin gwiwarku, da fatan za ku taimaka,” inji wasiƙar.

Jam’iyyar za ta fara sayar da fom ɗin takarar muƙamai daban-daban a ranar 22 ga watan Afrilu, sannan kuma za ta kare a ranar 7 ga watan Mayu.

Jam’iyyar APC ta kuma bayar da shawarar cewa fam ɗin na nuna sha’awar ’yan majalisun jihohin zai ci Naira 500,000, yayin da fam ɗin takarar zai ci Naira 1,500,000.

A ɓangaren kujerun majalisar wakilai kuwa, fom ɗin nuna sha’awa zai laƙume Naira miliyan 1 sannan fom ɗin tsayawa takara zai ci Naira miliyan 4, yayin da masu neman kujerar Sanata za su biya Naira miliyan 2 na fom ɗin takarar.

Kujerar gwamna kuwa, fam ɗin takarar zai lashe Naira miliyan 5 da kuma Naira miliyan 25 na fam ɗin takara. A matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, za a kashe fam miliyan 5, yayin da fam miliyan 40 na takarar.

A ranar Juma’a ne jam’iyyar ta tsayar da ranar 20 ga watan Afrilu domin gudanar da taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC).

A cewar jam’iyyar, taron zai yi la’akari da jadawalin zaɓen fidda gwani na zaɓen 2023 da sauran harkokin da suka dace.