2023: Atiku zai kawo ƙarshen matsalar tsaro idan ya zama Shugaban Ƙasa – Rabi’u Agaje

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Ɗan takarar majalisar jiha a Ƙaramar Hukumar Ƙiru a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar PDP, Hon. Rabiu Garba Agaje ya ce idan Atiku Abubakar ya zama shugaban ƙasa zai kawo ƙarshen rashin tsaro da tabbatarda kwanciyar hankali a ƙasar nan.

 Agaje ya ƙara da cewa tun daga ƙirlirar Jam’iyyar PDP da mulki da ta yi kowa ya ga irin adalcin da ta yi shi ya sa har yanzu mutane a koyaushe suke so ta dawo mulki a ƙasar nan domin a samu cigaba.

Agaje ya yi nuni da cewa idan PDP ta dawo mulki mutane da yawa za su dawo cikin hayyacinsu domin ita ce ta al’umma domin kawar da ƙangi da aka jefa mutane.

Ya ce yanzu yanda ake tafiyar da mulki a ƙasar nan akwai gazawa, ba a tafi da shi yadda ya kamata, kuma in Allah ya kai su ga nasara suna da yaƙinin cewa mutane za su yi na’am da irin mulkin da za su yi don za su duba fanni-fanni na halin da ƙasa suke ciki tun daga yanayi da makarantu ke ciki in ka je mazaɓu ka ga yanda ake tafiyar da makarantu a yanayi mara daɗi kasan abin kunya ne wasu ‘yan ƙasashen su zo Nijeriya su ga yadda ake tafiyar da makarantu da harkar lafiya.

Hon. Rabiu Garba Agaje ya ce takarar da yake yi ta al’umar Ƙiru ce su suka ga cancantar ya fito.

Ya yi kira ga al’umma akan su bada gudunmmuwa don kawo sauyi a yankin duba da yadda ɗimbin matasa ba su da aiki ga ma’aikata da suka gama aiki a wani matsanancin hali ba kuma abinda zai ceto Ƙiru da Jihar Kano baki ɗaya illa su fito su zaɓi PDP don a kawo gyara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *