2023: Ba Bala da Saraki ne ‘yan takarar shugaban ƙasar PDP na Arewa ba – Sule Lamiɗo

Daga AMINA YISUF ALI

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamiɗo ya ƙaryata rahotannin da suke ikirarin cewa, manyan Arewa sun fitar da Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed da kuma tsohon shugaban majalisar zartarwa, Bukola Saraki a matsayin ‘yan takara Shugaban ƙasa na raba-gardama da Arewa za ta tsayar a kakar zaɓe ta 2022, a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Lamiɗo, wanda ya gabatar da jawabinsa a wani taron manema labarai ya bayyana cewa, cewa, waɗancan rahotanni da suke ta zagawa ba ra’ayin manyan Arewa na jam’iyyar PDP ba ne, sai dai ra’ayin ƙashin kai na waɗanda suka haɗa rahoton.

Ya ƙara da cewa, har yanzu dai shugabannin PDP da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar ba su tsayar da wan ɗan takara na raba-gardama ba.

Lamiɗo kuma ya bayyana cewa, abinda ya sa ya saki wannnan bayani shi ne, yadda hankalin masu ruwa da tsaki na PDP a jihohin Arewa ya tashi a kan wasu rahotanni da suke nuna cewa, wasu daga cikin dattawan Arewa sun zavi wasu ‘yan takara guda biyu sanannu a matsayi ‘yan takarar shugabancin ƙasar nan a jam’iyyar PDP.

“Bayan tuntuɓar shugabannin jam’iyyar na jihohin Arewa guda 19 da na Birnin Tarayyar Abuja, nake sanar da sauran mambobin jam’iyyarmu, da sauran jama’a cewa rahotannin da suke yawo a kafafen yaɗa labarai ba komai ba ne illa ra’ayin son zuciya na waɗanda suka wallafa rahoton, amma ba matsayar mambobin jam’iyyar PDP na Arewa ba ne, inji shi.

A ƙarshe ya bayyana cewa, a yanzu haka dai ana kan tattaunawa da dukkan masu zawarcin kujerar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP da zummar samar da matsaya guda don gudanar da zaɓen shugabanni cikin maslaha. Kuma a cewar sa, wannan matsayar da aka ce manyan Arewa sun ɗauka, matsaya ce wacce za ta illata Arewa, har ma da ‘yan takarar da suka fito daga Arewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *