2023: Ba mu amince da saka sunayen Lawan da Akpabio a matsayin ‘yan takarar Sanata ba – INEC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), ta ce ba ta amince da saka sunan Sanata Ahmed Lawan matsayin ‘yan takarar sanata a Yobe ta Arewa da Godswill Akpabio a matsayin ɗan takarar sanata a Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma ba.

Hukumar INEC ta ce ba ta ɗauki ɗaya daga cikin mutanen biyu a matsayin ‘yan takarar Sanata a zaɓen 2023 mai zuwa ba.

Kwamishinan INEC na Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Kaɗa Ƙuri’a, Festus Okoye, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata mai taken: ‘zarge-zarge dangane da tantance ‘yan takara a wasu gundumomin sanatoci da aka gabatar wa ‘yan jarida.

Okoye ya ce a matsayin shaida na rawar da hukumar ta taka, tun da farko an gabatar da kwafin gaskiya na Fom 9C da jam’iyyun suka shigar kuma hukumar ta samu a ranar 17 ga Yuni, 2022 lokacin da aka rufe dandalin tantance sunaye.

Domin a fayyace, ya ce Fom EC9 shi ne fom ɗin sunayen ‘yan takara da jam’iyyun siyasa ta miƙa wa INEC kuma sune a tashar ta INEC.

Ya ce an yi nuni a fili a kan sunan fom ɗin da aka karva a ranar 17 ga watan Yuni, 2022 lokacin da aka rufe tashar.