Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba shi da ɗan takara ɗaya da zuciyarsa ta raja’a akan shi ya gaje shi.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a hira da ya yi da talbijin ɗin Channels TV a Abuja ranar Laraba.
”Ba ni da wanda na ke so ƙarara ya gaje ni a 2023, idan ma akwai to zan bar shi a can cikin zuciyata kawai domin idan na faɗi kila gobe a neme shi a rasa.”
Wa’adin mulkin Buhari zai kare ne a cikin shekarar 2023, wannan ya sa tun daga yanzu masu sha’awar maye gurbin sa ya san ya sauka suka fara ɗaura niyya.
A cikin kwanakin nan, ƙungiyoyi daban-daban sun riƙa fitowa suna tallata mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, cewa shine ya fi dacewa ya yi takarar kujerar shugaban ƙasa idan Buhari ya kammala wa’adin sa.
Sai dai kuma shi ma jigon jam’iyyar, Bola Tinubu ya daɗe yana nuna zai fito takarar shugaban ƙasa a 2023. Sai dai kuma dukkan su ba su bayyana ra’ayoyin su ba tukunna.
Haka kuma shi ma tshon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan akwai waɗanda suke ganin akwai yiwuwar zai canja jam’iyya ya dawo APC domin ta ba shi takarar shugaban ƙasa.
Har yanzu dai babu wanda ya fito daga cikin su ya bayyana ƙararar cewa yana son fitowa takarar shugaban ƙasa a 2023.
Ko ma dai wanene idan lokaci ya yi a gani, domin masu iya magana na cewa ‘jira ba ta buwaya.’