2023: Bakin alƙalami ya bushe kan batun sauya ’yan takara, inji INEC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta ce, ba za ta amince da janyewa ko sauya sheƙa ba bayan fitar da jerin sunayen ’yan takarar da za su tsaya takara a zaven 2023.

Sai dai hukumar ta ce, za a iya yin maye gurbin ne kawai idan mutum ya mutu kamar yadda sashi na 34(1) na dokar zaɓe ya tanada ko kuma bisa umarnin kotun da ta dace.

Gargaɗin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan na ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zace Barista Festus Okoye ya fitar a Abuja.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “a bisa sashe na 32 (1) na dokar zaɓe ta 2022 da kuma sashi na 8 na jadawalin da jadawalin ayyukan zaɓen 2023, hukumar a yau 4 ga Oktoba, 2022 ta fitar da jerin sunayen ’yan takarar zaɓen Jihohi (Gwamnati) da kuma mazaɓar Majalisar jiha.

“Buga cikakkun sunayen ’yan takarar da aka tsayar a zaɓen Jihohi ya biyo bayan yadda jam’iyyun siyasa suka gudanar da zaɓen fidda gwani da kuma kammala zaɓen fitar da gwani.

“Idan za a iya tunawa, a ƙarshen wannan tsari, jam’iyyun siyasa da suka gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani sun sanya jerin sunayen da kuma bayanan sirri na duk wanda aka zaca zuwa dandalin ’yan takara na Hukumar da kuma nunin da aka yi a mazavunsu a faɗin ƙasar nan kamar yadda sashi na 29(3) ya tanada na dokar zaɓe.

“Daga baya, ’yan takarar da aka tantance na gaskiya sun samu damar janye takararsu bisa raɗin kansu ta hanyar sanarwa a rubuce tare da kai irin wannan sanarwar ga jam’iyyar siyasar da ta tsayar da su zaven.

“Bayan haka, jam’iyyun siyasa sun maye gurbin irin waɗannan ’yan takara a ƙarƙashin sashe na 31 na dokar zaɓe wanda ranar ƙarshe ta kasance ranar 12 ga watan Agusta, 2022 domin gudanar da zaɓen Jihohi kamar yadda aka tanada ƙarara a sashi na 6 na Jaddawalin ayyuka da Hukumar.

“Bayan haka, ba a yarda a janye ko musanya ’yan takara sai idan mutum ya mutu kamar yadda sashe na 34 (1) na dokar zaɓe ya tanada ko kuma bisa umarnin kotun da ta dace.

“Jerin da aka buga a yau ya ƙunshi sunayen ’yan takarar da aka tantance masu inganci a zaɓen jihohi a ƙarshen zaben fidda gwani na jam’iyya da kuma lokacin da aka ware na janyewa da sauya ’yan takara.

“A taƙaice, jam’iyyun siyasa 18 sun tsayar da ’yan takara 837 da abokan takararsu a zaɓen gwamnoni 28 da zai faɗo a shekarar 2023. A zaɓen Majalisar Jiha, ’yan takara 10, 231 ne ke neman kujeru 993 na Majalisar Jiha.

“An buga jerin sunayen mazaɓu na musamman a kowace jiha inda suke yayin da aka shigar da cikakken jerin shafuka 894 na ƙasa baki ɗaya zuwa gidan yanar gizon Hukumar.

“Ana buƙatar jam’iyyun siyasa da su miƙa duk wani rahoto kan jerin sunayen ‘yan takara ga hukumar kuma dole ne shugaban da sakataren jam’iyyar na ƙasa ya sanya hannu.”

A halin da ake ciki, Majalisar Dattawa a Laraba ta tabbatar da tantance sunayen kwamishinonin zaɓe (REC) 19 ga hukumar INEC.

Haka kuma ta tabbatar da naɗin Muhammad Sabo Lamido a matsayin babban kwamishinan kuɗi da kuma asusu na hukumar kula da harkokin man fetur ta Nijeriya NUPRA.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *