2023: Dauda Lawal Dare ya sake zama ɗan takarar gwamnan Jihar Zamfara a PDP

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Bayan kammala zaɓen fidda gwanin ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara, an tabbatar da Dauda Lawal Dare a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri’u 422.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen fidda gwani na Jam’iyyar PDP reshen Jihar Zamfara da ke Gusau a ranar Juma’a, shugaban zaɓen da hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa ta turo don gudanar da zaɓen, Hassan Hyte kuma shugaban Kam’iyyar PDP na Jihar Kaduna, ya bayyana cewa abokan hamayyarsa su ne, Dr. Ibrahim Shehu wanda ya samu ƙuri’a ɗaya kacal, Hafiz shi ma ƙuri’a ɗaya.

Hassan ya ci gaba da cewa, jimillar ƙuri’u 255 ne aka kaɗa, yayin da wakilai 431 aka tantance su, sannan 428 suka kaɗa ƙuri’a, yayin da wakilai 3 ba su kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓen ba.

A cewarsa, an samu ƙuri’a guda 4 mara kyau, yana mai jaddada cewa an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da aminci.

“An gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci kamar yadda dokar jam’iyyarmu da kuma dokar kasa sula tanadar,” inji Hassan.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Gusau a makon da ya gabata ta soke zaɓen fidda gwani na takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara wanda ya kawo Dauda Lawal Dare a matsayin ɗan takarar gwamnan PDP na 2023 biyo bayan ƙarar da Engr Ibrahim Shehu ya shigar a gabanta, yana ƙalubalantar sahihancin zaɓen fidda gwanin a jihar.

A jawabinsa jim kaɗan bayan kammala zaɓen, shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Zamfara, Dr. Ahmed Sani Ƙaura ya bayyana jin daɗinsa kan yadda zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali tare da yaba wa shugabannin jam’iyyar na ƙasa bisa goyon bayan da suka bayar wajen ganin an gudanar da zaɓen cikin nasara.