Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Kudu kuma Gwamnan Jihar Ondo, Mista Oluwarotimi Akeredolu, a ranar Talata, ya yi gargaɗin cewa, duk jam’iyyar da ta kuskura ta sanya ɗan Arewa a matsayin ɗan takarar Shugaban Ƙasa a shekarar 2023, to za ta faɗi ƙasa warwas.
Gwamna Akeredolu ya bayyana cewar gwamnoni a yankin Arewa na ƙasar dake ƙarƙashin inuwar Ƙungiyar Gwamnonin Kudu a shirye take domin tabbatar da cewa shugaban ƙasa ya fito daga yankin Kudu.
Gwamnan ya bayyana haka a ofishin sa a lokacin da ‘ya’yan jam’iyyar suka kawo masa ziyara masu rajin maida mulki a yankin Kudu ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar Dr. Pogu Bitrus.
Gwamnan wanda suke sukar tsarin karɓa-karɓa suna kawo matsala a kasancewar Nijeriya, domin ya yi imani a adalci.