2023: INEC ta fitar da sabuwar dokar sharaɗin lashe zaɓen Gwamna a Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI

Wanda zai lashe zaɓen shugaban ƙasa, tilas ya samu ƙuri’un mafiya rinjaye a ɓangarorin da ake buƙatar aƙalla kaso 2 cikin uku na gabaɗaya ƙuri’un jihohi 36 da suke a Nijeriya. Hukumar zaɓen ce mai zaman kanta ta Nijeriya ta bayyana hakan. Tare da bayyana cewa, wannan doka tana ƙunshe ne a dokar zabe ta 2022 wacce dokar zabe ta 1999 ce aka yi wa garambawul.

Kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitin ba da bayanai da ilimtar da masu zaɓe na hukumar INEC,  Mista Festus Okoye shi ya bayyana haka. 

Mista Okoye ya bayyana hakan ne ranar Litinin ɗin da ta gabata a jihar Legas a wani taron ƙara wa juna sani na horas da ‘yan jaridu don shirya wa zaɓen shekarar 2023 mai zuwa da kuma wasu manyan bayanai game da sababbin dokokin zaɓe na 2022. 

Mista Okoye ya ƙara da cewa, za a sake sabon zaɓe tsakanin wanda ya fi yawan ƙuri’u na bai ɗaya da wanda ya fi yawan ƙuri’u wanda ya kawo kaso jihohin da ake buƙata. Kuma ba dole ne ya zama shi ne na biyu ma fi yawan ƙuri’u a gabaɗaya zaɓen ba. 

Hakazalika a cewar sa, shi ma zaɓen Gwamna, sammakal. Domin shi ma wanda zai lashe zaɓen shi ne wanda ya samu lashe ma fi yawan ƙuri’u da kuma kaso biyu cikin uku na dukkan ƙuri’un da aka kaɗa a dukkan ƙananan hukumomin da suke a ƙarƙashin jiharsa. 

Idan ɗan takara ya kasa kawo dukkan ƙuri’un da aka sharɗanta masa, za a sake sabon zaɓe a tsakanin mafi yawan ƙuri’un da kuma ma fi yawan mamayar ƙananan hukumomin. ‘Yan takarar su biyu kacal ne za su bayyana a takardar zaven a zaɓe na biyu na raba gardama, idan buƙatar hakan ta taso, a cewar sa.

Ɗan takarar shugaban ƙasar kuma, wanda ya lashe mafi yawan ingantattun ƙuri’u daga dukkan jihohi 36 na tarayyar Nijeriya shi ne zai zama zakara. 

Hakazalika, Kwamishinan na  INEC  ya bayyana cewa, dokar zaven ta ƙara ɗabbaƙa fasahar zamanin wacce Kwamishinan ya samar.

Haka kuma a cewar sa, hukumar INEC ta farlanta amfani da na’urar tantance masu dangwala ƙuri’a (SCRM), wanda a baya amfani da na’urar tantancewar ba farilla ba ne, kawai zaɓi ne da hukumar ta bayar.

A cewar sa, wannan na’ura ta tantance mai zaɓe, an yi ta ne musamman saboda  a tabbatar da an samu sahihin zame na adalci. Wannan ita ce babbar manufar da ta sa INEC ta ƙirƙiro wannan na’urar.

Haka dai a gyaran da aka yi wa dokar zaɓen shi ne, kuskure a alamar jam’iyya ba ya lalata ƙuri’a. Kuma hukumar ta yi kira ga jam’iyyu da su zo su duba logon jam’iyyunsu a hukumar kafin nan kafin lokacin zaɓen.  

Haka wanda ya taimaka wa ɗan takara wajen maguɗin zaɓe, ya karya dokar zaɓe ta sashe na 92(5) wanda ya haramta amfani da ƙarfi ko ta da tarzoma yayin zabe, wanda hukuncinsa shi ne, biyan tarar Naira dubu ɗari biyar ne ko zaman gidan kaso na shekara 3 ko kuma a haɗa masa dukkan. 

Haka duk wasu ‘yan takara ko wani mutum ko wasu gungun mutane. Da suka yi amfani da ƙarfi ko yaudara su ma sun karya doka kuma za a yi musu hukuncin da dokar zaɓe ta sashe na 93 ta tanadar wa masu laifi irin nasu. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *