2023: INEC ta yi wa jam’iyyu muzurai kan wa’adin zaɓen fidda gwani

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya, INEC, ta soma yi wa jam’iyyun siyasa muzurai, inda ta ce ta na nan a kan matsayinta na wa’adin ranar 3 ga watan Yuni, 2022, don jam’iyyu su kammala zaɓukan fitar da gwani.

Sai dai, jam’iyyun ƙasar ta bakin majalisar tuntuɓa tsakanin jam’iyyu sun ce wa’adin ya takura musu, duk da yake buƙatarsu ba ta saɓa wa tsarin mulki ba.

A hirarsu da BBC Shugaban majalisar jam’iyyun, Injiniya Yabagi Sani ya bayyana dalilinsu na neman hukumar zaven ta ƙara musu wa’adi.

Ya ce tun da ita kanta dokar sabuwa ce, ya kamata INEC, ta duba buqatar tasu, domin suna gudun kada su yi abu cikin gaggawa kuma a zo a samu wata jayayya ta shari’a a kotu.

Ya qara bayani da cewa, ”to shi ne ya sa muka kira ita hukumar zaɓe cewa don Allah su sake dubawa su ga yadda za a yi a ba jam’iyyu, a ba mu lokaci har zuwa Agusta ba Yuni ba, a ƙara mana wata biyu tun da bai shiga abin da dokar ƙasa ta ce ba, bai tava wannan wata shida da kundin mulki ya tanada ba.”

To amma kuma Injiniya Yabagi ya ce, da suka gabatar wa da shugaban hukumar zaɓen wannan buƙata, ya shaida musu cewa idan har suka sauya, abin zai iya haifar musu da matsaloli.

Amma ya ce shugaban ya yi musu alqawrin cewa za su je su duba buƙatar.

Shugaban majalisar jam’iyyun na Nijeriya ya jadda muhimmancin ganin hukumar zaɓen ta amsa wannan buqata ta su yana mai nuni da cewa ita hukumar ai mai sa ido ce kawai domin tabbatar da komai ya gudana yadda ya dace.

”Su dai nasu a matsayinsu na hukuma su ga cewa an yi zaɓen a bisa doka, amma zaɓen ainahin zaɓen, ai jam’iyyu ne za su yi ba su za su yi ba,” inji shi.

To, sai dai a ƙarin bayanin da ta yi wa BBC, mai magana da yawun hukumar zaɓen ta Nijeriya, Hajiya Zainab Aminu, ta jaddada cewa ƙara wa’adin zai iya rikita jadawalin zaɓen da hukumar ta riga ta fitar, saboda haka INEC na kan bakanta.

Ta ce, sai biyu a cikin sati biyu da ya gabata hukumar ta zaɓe ta yi wa jam’iyyu tuni a kan muhimmancin kiyayewa da jadawalin zaɓe na 2022 musamman ma batun fitar da ‘yan takara, dokar da ta riga ta fitar tun ranar 26 ga watan Fabrairu na 2022.

Jami’ar ta INEC, ta yi nuni da cewa har kullum hukumarsu tana aiki ne da dokokin zaɓe na 2022:

”Wanda kuma idan aka duba sashe na 29, sakin layi na ɗaya, doka ta tanadar da dukkan jam’iyyun siyasa su aike da sunayen ‘yan takarkarinsu da suka tsaida bayan gudanar da zaɓuka na cikin gida kafin kwanaki 180 g ranar babban zave,”‘ inji ta.

A ƙarshe mai magana da yawun INEC ɗin ta ce, hukumar zaɓen tana nan a kan bakanta, kuma ta jaddada buƙatar ganin jam’iyyun na Nijeriya sun ci gaba da gudanar da shirye-shiryensu, tare da gudanar da zaɓen fitar da ‘yan takararsu kamar yadda aka tsara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *