2023: Jonathan ya ƙaryata komawarsa Jam’iyyar APC

*Ya ce, saya masa fom tozarci ne

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya, Dr. Goodluck ya musanta sani da umarnin saya masa takardar neman shiga tsayawa takarar shugabancin ƙasa ta Naira miliyan ɗari a zaɓen shekara ta 2023, yana cewar, yin hakan wani tozarci ne ga mutumtakarsa.

Mataimaki na musamman akan lamuran yaɗa labarai wa tsohon shugaban ƙasan, Ikechuku Eze ya bayyana cewar, duk da yabawar tsohon shugaba dangane da ɗimbin kiraye-kiraye da aka yi masa na shiga cikin takarar shugabanci a shekara ta 2023, Jonathan bai amince da waɗannan buƙatu ba.

“Muna da masaniyar wani gungun jama’a wai ya sayi takardar tsayawa takarar neman shugabanci na jam’iyyar APC da sunan tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan. Muna so mu fayyace ƙarara cewar, Dr. Jonathan bai san da wannan magana, kuma bai umarci yin hakan ba.

“Muna so mu shaidar cewar, idan tsohon shugaban ƙasan yana buƙatar tsayawa takarar zaɓe, zai bayyana aniyar sa a fili, kuma ba zai shiga ta hanyar da ba ta dace ba, ko ta ƙofar baya ba.

“Sayen takardar neman shiga takarar zaɓe da sunan Dr. Jonathan ba tare da sanin sa ba, idan an yi la’akari da matsayin da ya riqe a ƙasar nan, yin hakan wani tozarci ne ga mutumtakarsa. Ya kamata jama’a su yi watsi da wannan batu.”

A ranar Litinin ce da ta gabata, wani gungun jama’ar Fulani, haɗi da almajirai, bayan sayar da wasu shanu, suka sayo takatar shiga takarar neman zabɓen shugaban ƙasa na jimlar kuɗi Naira miliyan ɗari na jam’iyyar APC wa tsohon shugaban ƙasa Jonathan.

A wani cigaban kuma, wani mai magana da yawun Shugaba Buhari, Bashir Ahmad a ranar ta Litinin ɗin ce ya sanar da ficewar tsohon shugaba Jonathan daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa jam’iyyar APC, haɗi da tabbatar da sayan takardun shiga takarar zaɓe.
Ahmad, wanda mataimaki ne na musamman ga Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari akan kafofin watsa labarai na zamani, ya rubuta a cikin yanar sanarwar sa ta tiwita cewar, “saboda haka, Goodluck Jonathan ya yi watsi da jam’iyyarsu ta adawa, kuma yanzu mamba ne a babbar jam’iyyarmu ta APC.”

Kuma da yake yi wa manema ƙarin bayani ta wayar salula, Ahmad ya ce a yanzu dai dukkan alamu sun nuna cewar, tsohon shugaban ƙasan ya nuna a zahiri zai sake tsayawa takarar neman shugabanci a ƙarƙashin tutar jam’iyyar da ta wancakalar da shi daga ofis shekaru bakwai da suka gabata.

Kamar yadda ya lura, jam’iyyar siyasa za ta sayar da takardar neman shiga takara ne kaɗai wa mambanta mai rajista, yana mai ƙarawa da cewar, babu wani mahaluki da zai biya zunzurutun kuɗi Naira miliyan ɗari ba tare da ya san dalilin ɓatar su ba.

“Babu wani mahaluƙi da zai fitar da maƙudan kuɗaɗe Naira miliyan ɗari na takardar tsayawa takarar shugabancin ƙasa daga wata jam’iyyar siyasa da shi ba mamba ba ne,” a cewar Ahmad.

Tunda farko dai a ranar ta Litinin da ta gabata, bayanai sun doge kafafan watsa labarai cewar, wani gungun jama’a da aka yi wa laƙabi da tawagar Fulani ce, ta sayi takardun tsayawa takarar neman shugabancin na Naira miliyan ɗari ƙasa da sunan Dokta Goodluck Jonathan.

Idan za a iya tunawa dai, a ranar 22 ga watan Afrilu data gabata, wata tawagar ‘yan Nijeriya ta yi zanga-zangar lumana, inda ta yi tattaki zuwa wani ofis na Jonathan dake Abuja inda ta roƙe shi ya tsaya takarar neman shugabancin ƙasa a 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *