2023: Jonathan ya ɗabbaƙa takarar shugabancin ƙasa ta Gwamna Bala

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Tsohon Shugaban Ƙasar Tarayyar Nijeriya, Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya amince da shaidar takarancin neman shugabancin ƙasar nan da Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed yake yi, yana mai bayyana Gwamna Bala da cewar, mutum ne mai tsantsar haƙuri, tawali’u da kuma sauraron kasancewar Nijeriya kyakkyawar ƙasa da inganci.

A wani jawabi da mataimaki ga gwamnan kan hulɗa da kafofin yaɗa labarai ta intanet, Lawal Muazu Bauchi, ya ce Dr. Goodluck Jonathan ya yi wannan furuci ne a ranar Alhamis da ta gabata, yayin da yake yi wa Gwamna Bala marhabun a gidan sa dake birnin tarayya ta Abuja, yana mai shaidar wa Gwamnan Bauchi Bala yana ɗaya daga cikin ministocin sa haziƙai masu yin aiki tuƙuru.

Goodluck Ebele Jonathan ya kuma yi matuqar yaba wa Bala Abdulkadir Mohammed bisa rashin yanke zumuncin sa da shi har zuwa wannan rana da ba ya kan karagar mulki, yana mai cewar, zai ji daɗin ganin ɗaukakekkiyar Nijeriya tare da shugaba mai tausayi, haziƙi, jajirtacce da ƙwararren shugaba matuƙar an bai wa Bala damar jagorancin wannan babbar ƙasa da tafi kowacce yawan jama’a a nahiyyar Afurka.

Ya kuma bayyana cewar, babu wata shakka Bala Abdulkadir Mohammed zai tabbatar da cikar muradun ‘yan Nijeriya, la’akari da ɗimbin nasarori da ya cimma lokacin da yake riƙe da kujerar ministan babbar birnin tarayya ta Abuja, da kuma nasarorin da ya cimma cikin shekaru uku da kasancewar sa gwamnan jihar Bauchi.

Goodluck Jonathan ya ce a matsayin sa na adali kuma kamilallen Uba, yana da ƙarfin gwiwar Bala Mohammed zai bai wa maras ɗa kunya ta hanyar nuna wa ‘yan Nijeriya kyakkyawan jagoranci abun koyi ga wasu.

Jonathan ya yaba wa gwamnonin Bauchi, Ribas da Taraba, Bala Mohammed, Nyesom Wike da Darius Ishaku bisa mutunta shi da jihar sa da suka yi, yayin da suka gayyace shi jihohin su inda walau dai ya ƙaddamar ko aza harsashin ayyukan cigaban jama’ar su, sai ya yi kira ga takwarorin gwamnonin da su yi koyi na irin wannan karamci da mutumtaka wa shugabanni ko jagorori na wannan ƙasa.

Da yake yin jawabin sa tun farko, Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya bayyana cewar, ya ziyarci gidan tsohon shugaban ƙasa ne tare da tawagar sa domin neman tubarraki, kuma ya sanar da shi aniyar sa ta shiga takarar neman shugabancin Nijeriya a zaɓen gamagari na shekara ta 2023 idan Mahalicci ya kai mu.

Gwamna Bala Mohammed ya kuma bayyana cewar, tarihin siyasar Nijeriya ba zai mance da Goodluck Jonathan ba, sadaukantakarsa, da kuma jajircewar sa na ganin daidaituwar ƙasa, haɗi da ƙwazon sa na ganin gudanar da zaɓe maras ruɗani da tashintashina.

Wani da yake cikin tawagar gwamnan kuma shehin malami, Farfesa Udenta O. Udenta ya ce ɗaukacin ‘yan Nijeriya suna da ƙwarin gwiwar cewa, Bala Mohammed, la’akari da aniyar sa ta son haɗin kai, tafiyar tarayya, kyautata wa, adalci, zaman lafiya, cigaba da bunƙasar ƙasa, zai fitar da kitse daga wuta.