2023: Kar ku zaɓi masu yanka filin masallatai – Gargaɗin Kahlifa Sunusi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Khalifan Tijjaniya, kuma tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi Lamido na II a wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zumuntar zamani an hango Muhammadu Sanusi Lamido yana bai wa masu zave shawara kan yadda za su jajirce wajen zaɓen waɗanda suke so ba wanda ya kwashe musu kuɗi ba.

Lamido yana cewa ka da mutane su zaɓi mutanen da za su kwashe musu kuɗinsu, “mutum ya shekara huɗu yana sayar da filayenku, yana sayar da masallatai, yana sayar da makabartunku, yana sayar da makarantunku, yana sayar da ganuwarku da asibitocinku ya tara kuɗi ya zo kuma ya sayi ƙuri’u da su.”

Maganganun na Muhammadu Sanusi Lamido sun ja hankalin jama’a, inda wasu ke ganin wannan saƙo ne na kai tsaye ga gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda ake zargin gwamnatin da cefanar da wasu filaye mallakin gwamnatin jihar.

A shekara ta 2020 ne Gwamna Ganduje ya tsige Sarki Muhammadu Sanusi II bisa zargin rashin ɗa’a ga gwamnati da kuma rashin sanin darajar masarauta