2023: Ku guji zaɓen masu ƙaryar an saya musu fom – Obasanjo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Shugaban Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya nemi ‘yan Nijeriya su raba kansu da zaɓen masu neman takarar da suke yi wa jama’a ƙarya.

Olusegun Obasanjo yana mai kira ga al’umma su guji kaɗa ƙuri’a ga duk wanda ke da’awar wasu suka saya masa fom ɗin takara.

Daga cikin masu neman kujerar shugaban ƙasa da suka yi iƙirarin masoya ne suka kawo masa fom ɗin shiga takara, akwai Alhaji Atiku Abubakar na PDP.

Rahoton ya ce sauran wanda ke taƙamar kyauta aka kawo masu fom sun haɗa da Gwamnan Sakkwato, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal da Peter Obi.

Akwai Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki. Kuɗin dukkansu bai yi ciwo wajen shiga takara ba.

Wazirin Adamawa ya riƙe kujerar tsohon mataimakin shugaban ƙasa a gwamnatin PDP, daga baya ya samu saɓani da mai gidansa kafin a shirya a 2019.

Obasanjo ya bayyana haka da yake jawabi a wajen bikin da aka shirya a kan rawan da jagororin Kirista suka taka sa’ilin da aka samu kai a mawuyacin hali.

An shirya wannan taro na musamman ne domin taya Fasto Itua Ighodalo murnar cika shekara 61. Obasanjo ya na cikin waɗanda suka yi jawabi a wajen bikin.

A cewar Obasanjo, babbar matsalar ƙasar nan ita ce shugabanci, ya ce qwararrun masana aka ɗauko kafin a tsara kundin tsarin mulkin da ake amfani da shi.

Obasanjo ya bayyana cewa, da za a samu shugabannin ƙwarai, da duk komai zai dawo daidai, Nijeriya za ta tafi kan turba madaidaiciya.

Dattijon ya ce duk mai cewa kyauta aka kawo masa fom, ba abin yarda ba ne.

“Yau ana biyan Naira miliyan 40. Wasunsu (‘yan takara) su na cewa matasa ne suka saya masu. Kai! Duk wanda ya faxa maku wannan ƙarya yake yi, ka da ku zaɓe shi.

“Wasu matasan su ka tara Naira miliyan 40? Idan za ku saye fom, ku saya ku faɗa mana. Babu dalilin yi mana ƙarya,” cewar Obasanjo.